Yanzu-yanzu: An dakatad da sanar da sakamakon Kogi zuwa gobe, APC na gaba da tazarar 205,633

Yanzu-yanzu: An dakatad da sanar da sakamakon Kogi zuwa gobe, APC na gaba da tazarar 205,633

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta dakatad da sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Kogi zuwa ranar Litinin, 18 ga Nuwamba, 2019 misalin karfe 8 na safe.

Baturen zaben jihar Kogi, wanda ya kasance shugaban jam'iyyar Ahmadu Bello ABU Zariya, Farfesa Ibrahim Umar, ya sanar da hakan Lokoja, babbar birnin jihar Kogi.

Farfesa Umar ya bayyanawa wakilan jam'iyyu da masu ruwa da tsaki su dawo gobe Litinin.

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kan gaba a zaben a jihar inda tserewa da jam'iyyar hamayya, Peoples Democratic Party (PDP), da tazarar 205,633 a sakamakon kananan hukumomi 19 cikin 21 da aka sanar.

Yayinda Dan takarar APC, Yahaya Bello, ya samu kuri'u 373,783 , Musa Wada na PDP yana da kuri'u 168,150

Kawo yanzu, INEC ta sanar da sakamakon kananan hukumomin Okene, Okehi, Adavi, Omala, Ijumu, Ogori/Magongo, Igalamela Odolu, Kabba Bunu, Koton Karfe, Olamaboro, Yagba East, Yagba West, Mopa Muro, Idah, Ajaokuta, Ifu, Dekina, Bassa, Ankpa

Sakamakon da za'a sanar gobe sune karamar hukumar Ibaji da Lokoja.

A bangare guda, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kan kafa tarihi a jihar Bayelsa yayinda take gaba da jam'iyyar hamayya, Peoples Democratic Party (PDP), da tazarar 86,330 a sakamakon kananan hukumomi shida cikin takwas na jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel