Bayelsa: APC na kan gaba da tazarar kuri'u 86,330 a kananan hukumomi 6 cikin 8

Bayelsa: APC na kan gaba da tazarar kuri'u 86,330 a kananan hukumomi 6 cikin 8

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kan kafa tarihi a jihar Bayelsa yayinda take gaba da jam'iyyar hamayya, Peoples Democratic Party (PDP), da tazarar 86,330 a sakamakon kananan hukumomi shida cikin takwas na jihar.

Yayinda Dan takarar APC, David Lyon, ya samu kuri'u 206,260, Duoye Diri na PDP yana da kuri'u 119,330.

Kawo yanzu, hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta sanar da sakamakon kananan hukumomin Yenagoa, Ogbia, Brass, Nembe, Kolokuma/Opokuma da Sagbama.

Sakamakon da ake saurara yanzu sune karamar hukumar Southern Ijaw da Ekeremor.

An tafi hutun rabin lokacin awa daya kafin a cigaba.

A wani labarin daban, Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta INEC ta ce an gano ma'aikatan wucin gadinta 30 da suka ce an sace sakamakon rikici da ya barke a karamar hukumar Olamaboro a zaben gwamnan jihar ranar Asabar.

Mai magana da yawun shugaban hukumar INEC, Rotimi Oyekanmi, a jawabin da ya saki ranar Lahadi a Abuja ya ce an gano dukkansu kuma suna cikin koshin lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel