Rundunar 'yan sanda ta bayyana adadin mutanen da suka mutu a zaben Kogi, INEC ta saki karin sakamako

Rundunar 'yan sanda ta bayyana adadin mutanen da suka mutu a zaben Kogi, INEC ta saki karin sakamako

A ranar Lahadi ne rundunar 'yan sanda a Lokoja ta tabbatar da cewa mutane uku ne suka rasa ransu yayin zaben gwamna da aka gudanar a jihar Kogi ranar Asabar.

Da yake tabbatar da hakan ga manema labarai, kwamishinan 'yan sandan jihar Kogi, Mista Akeem Busari, ya ce har yanzu rundunar 'yan sanda tana cigaba da tattara rahoto a kan zaben domin sanin hakikakanin adadin mutanen da suka mutu ko suka samu rauni sanadiyar zaben.

Busari ya kara da cewa a kalla 10 ne suka samu raunuka a sassan jihar ta Kogi yayin zaben gwamnan.

Ya bayyana cewa mutanen uku sun mutu ne sakamakon harin da wasu 'yan bindiga suka kai a wata cibiyar kada kuri'a da ke makarantar firamare ta St. Luke da ke unguwar Adanakolo.

Busari, duk da haka, ya bayyana cewa akwai zama lafiya a jihar, kuma komai yana tafiya daidai a halin yanzu.

Kazalika, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da sakamakon zabe daga wasu karin kananan hukumomin jihar Kogi 8.

Sakamakon zaben ya nuna cewa, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, dan jam'iyyar APC yana da kuri'u 36,954 a karamar hukumar Okehi, yayin da dan takarar jam'iyyar PDP, Mista Musa Wada, ya samu kuri'u 478 kacal.

DUBA WANNAN: Dino Melaye ya sha kaye a kananan hukumomi 4 cikin 6 kamar yadda INEC ta sanar

A karamar hukumar Ajaokuta, Bello ya samy kuri,u 17,952 yayin da Wada ya samu kuri'u 5,565.

Bello ya samu kuri'u 4,953 a karamar hukumar Mopa yayin da Wada ya samu kuri'u 3,581.

Sakamakon zabe karamar daga karamar hukumar Idah ya nuna cewa Bello ya samu kuri'u 4,602 yayin da wata ya samu kuri'u 13,962.

A sakamakon karamar hukumar Olamaboro, Bello ya samu kuri'u 16,876 yayin da Wada ya samu kuri'u 8,155.

Bello ya samu kuri'u 7,868 a karamar hukumar Yagaba ta yamma yayin da Wada ya samu kuri'u 8,860.

Ya zuwa yanzu hukumar INEC ta saki tare da sanar da sakamakon zabe a kanana hukumomi 16 daga cikin 21 da jihar Kogi ke da su.

(NAN)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel