Wada ya lallasa Jam’iyyar APC mai mulki a cikin karamar hukumar Omala

Wada ya lallasa Jam’iyyar APC mai mulki a cikin karamar hukumar Omala

‘Dan takarar Jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi, Injiniya Wada Musa, ya samu nasara a karamar hukumar Omala. Jam’iyyar adawar ta samu kuri’un da su ka kusa ribanya na APC.

Kamar yadda hukumar zabe na INEC ta tabbatar, jam’iyyar PDP ce ta karbe Omala da kuri’a 14, 403. APC mai mulkin jihar ta zo ta biyu da kuri’u 8, 473. Jam’iyyar SDP ta tashi a ta uku da kuri’u 567.

Haka zalika Wada Musa na PDP ya yi galaba a kan ‘Dan takarar jam’iyyar APC, Gwamna mai-ci Yahaya Bello a karamar hukumar Ankpa. Jam’iyyar PDP ta samu gagarumar nasara a Garin.

Musa ya lashe kuri’u 28, 108, yayin da Bello ya biyo baya da kuri’u 11, 269. Masu hasashe sun bayyana cewa zai yi wahala dama jam’iyyar APC da Yahaya Bello su iya kai labari a Yankin.

Sauran inda ake zargin kudi ya yi aiki sun hada da Adavi, Ibaji, Itale Iyanu, Idah, Kogi, da kuma Garin Ajaokuta. Ana kuma zargi jami’an tsaro da yin katsalandan cikin harkar zaben jihar.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta tashi da karfi a zaben Gwamnan Jihar Bayelsa

Sakamakon zaben na 2019 ya nuna cewa mutum 142, 912 ne aka yi wa rajista a Ankpa. Daga cikinsu an tantance mutane 41, 980, wanda aka samu 41, 345 da su ka fita su ka kada kuri’arsu.

‘Yar takarar Jam’iyyar SDP, Natasha Akpoti, ta samu kuri’u 399 a Garin. ‘Yar takararce ta zo ta uku a bayan manyan jam’iyyun. ‘Yan takara 24 ne su ka fito su na harin kujerar gwamnan jihar.

Kungiyar YIAGA ta fito ta na kokawa da cewa an tafka ba daidai ba a zaben na 16 ga Watan Nuwamba. Kungyar mai zaman kanta, ta ce akwai alamun tambaya game da wannan zaben.

Daga cikin inda kungiyar ta ke zargin an yi magudi akwai Ankpa. YIAGA ta ce an yi amfani da kudi wajen sayen kuri’un jama’a a wasu rumfunan zabe da ke Mazabar Ankpa da sauran wurare.

Sauran inda ake zargin kudi ya yi aiki sun hada da Adavi, Ibaji, Itale Iyanu, Idah, Kogi, da kuma Garin Ajaokuta. Ana kuma zargi jami’an tsaro da yin katsalandan cikin harkar zaben jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Online view pixel