Yanzu-yanzu: An ga jami'an INEC 30 da akayi garkuwa da su a Kogi

Yanzu-yanzu: An ga jami'an INEC 30 da akayi garkuwa da su a Kogi

Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta INEC ta ce an gano ma'aikatan wucin gadinta 30 da suka ce an sace sakamakon rikici da ya barke a karamar hukumar Olamaboro a zaben gwamnan jihar ranar Asabar.

Mai magana da yawun shugaban hukumar INEC, Rotimi Oyekanmi, a jawabin da ya saki ranar Lahadi a Abuja ya ce an gano dukkansu kuma suna cikin koshin lafiya.

Yace: "Muna tabbatar muku da cewa ma'aikatan wucin gainmu 30 da aka tura zaben Kogi a rumfar zabe 002, 006 and 013 a Olamaboro III da rumfuna zabe 006, 012, 015, 016, 022 a Imani 1, dukka a karamar hukumar Olamaboro, sun fito."

"Suna cikin koshin lafiya kuma sun koma gidajensu. Shugaban hukumar ya yi magana da wasu daga cikinsu da kana kuma sun tabbatar da cewa suna lafiya."

Yanzu-yanzu: An ga jami'an INEC 30 da akayi garkuwa da su a Kogi
Yanzu-yanzu: An ga jami'an INEC 30 da akayi garkuwa da su a Kogi
Source: Facebook

Yanzu-yanzu: An ga jami'an INEC 30 da akayi garkuwa da su a Kogi
Yanzu-yanzu: An ga jami'an INEC 30 da akayi garkuwa da su a Kogi
Source: Twitter

Source: Legit

Tags:
Online view pixel