Kogi: Musa Wada ya ce bai aminta da sakamakon zabe ba

Kogi: Musa Wada ya ce bai aminta da sakamakon zabe ba

Tun kafin sanar da dukkan sakamakon kananan hukumomin da ke jihar Kogi da aka yi zabe a jiya Asabar, dan takarar jam'iyyar PDP, Musa Wada ya ce bai aminta da sakamakon ba.

A yayin zantawa da manema labarai a garin Lokoja a ranar Lahadi, wanda a lokacin ne ake sanar da sakamakon zaben na kananan hukumomi 21 na jihar, Wada ya zargi cewa sakamakon duk na bogi ne.

Ya ce, abinda ya faru a jihar a cikin ranakun karshen makon ya yi karantsaye ga damokaradiyya da kuma burin mutanen jihar Kogi.

Ya ce, abinda ya faru yayin zaben bai bayyana gaskiyar ra'ayin mutane jihar ba.

Ya kara da jajanta yadda jami'an tsaro suka hada kai da hukumar zabe mai zaman kanta don dakile ra'ayin mutanen jihar Kogin.

DUBA WANNAN: Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar tseratar da mata da kananan yara daga 'yan Boko Haram

Ya ce babu bukatar zabe, "Idan har Okene da ke da tantattun masu kada kuri'a dubu arba'in zasu kawo kuri'u dubu dari da sha biyu." Ya ce wannan mummunar rana ce ga mutanen jihar Kogi don kuwa suna ta makoki.

"Wa kuka ga yana murna? Haka take kasancewa bayan nasara? Ba don ni bane, don mutanen jihar kogi ne da ke cikin mummunan hali na shekaru hudu," ya ce.

"Na lashe zaben da aka yi cikin gaskiya. Kalli yadda suka bar guraren da aka yi magudi kamarsu Okene. Akwai wurare da yawa da aka kwace akwatunan zabe. Da anyi abinda ya dace, ba shakka ni zan lashe zaben," ya bayyana.

Kamar yadda yace, jam'iyyar APC ta maida Najeriya halin da ta ke ciki a da.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel