APC ta yi nasara a karamar hukumarsu Jonathan, INEC ta sanar

APC ta yi nasara a karamar hukumarsu Jonathan, INEC ta sanar

Jam'iyyar APC ta yi nasara a karamar hukumar Ogbia ta jihar Bayelsa a zaben da aka yi a ranar Asabar. Otueke na karkashin karamar hukumar Ogbia, garin tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan.

A karamar hukumar Ogbia, APC ta samu kuri'u 58,016 inda jam'iyyar PDP ta samu 13,763.

An sanar da sakamakon zaben karamar hukumar ne da ranar yau Lahadi.

Kiris ya rage shugaban karamar hukumar, Ebinyo Turner, ya kawo tsaiko a tattara kuri'un a safiyar Lahadi. Shugaban karamar hukumar ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da hada kai da APC don rubuta sakamakon bogi.

Daga baya ne sojoji suka cafke shugaban karamar hukumar don kawo maslaha.

Karamar hukumar Ogbia na da gunduma 13 kuma duk jam'iyyar APC ce ta yi nasarar lashesu.

DUBA WANNAN: Dino Melaye ya sha kaye a kananan hukumomi 4 cikin 5 kamar yadda INEC ta sanar

A gundumar Otueke, APC ta lashe dukkan akwatunan zabe har da wanda tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya kada kuri'a.

Dan takarar jam'iyyar APC shine David Lyon mai shekaru 49, amma tsohon minista Heinekan Lokpori na kalubalantar takararsa.

Dan takarar jam'iyyar PDP kuwa shine Duoye Diri mai shekaru 60 a duniya. Ya samu goyon bayan Gwamna Seriake Dickson.

An gano cewa, Jonathan ya janye goyon bayansa ga jam'iyyarsa a jihar bayan rashin jituwar da ke tsakaninsa da Gwamna Dickson akan kalubalantar takarar Duoye Diri da ya yi.

Baya ga karamar hukumar Ogbia, APC ta kawo karamar hukumar Nembe, tushen abokin takarar Lyon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel