Kogi 2019: Jam’iyyar APC ta doke PDP a Kakanda, Yagba da Kabba

Kogi 2019: Jam’iyyar APC ta doke PDP a Kakanda, Yagba da Kabba

Mun samu labari daga hukumar NAN na kasa cewa karamar Ministar babban birnin tarayya Abuja, Ramatu Tijjani Aliyu ta taimawa jam’iyyar APC wajen lallasa PDP a zaben gwamnan Kogi.

Jam’iyyar APC mai mulki ce ta lashe akwatunan Garin Yagba da Kakanda inda nan ne Dr. Ramatu Tijjani Aliyu ta fito. Tijjani Aliyu ce mataimakiyar Ministan Abuja a gwamnatin shugaba Buhari.

‘Dan takarar majalisar dattawa na shiyyar na yammacin Kogi, Smart Adeyami ya yi galaba a kan Sanata mai-ci Dino Melaye wanda ya samu kuri’u 4, 907, ‘dan takararadawar ya samu kuri’a 2,013.

Kafin nadin Dr. Tijjani Aliyu a matsayin Ministar Abuja, ita ce shugabar mata na jam’iyyar APC na kasa. Kuma har yanzu ta na da tasiri a siyasar jihar Kogi inda ta taimakawa APC a zaben jiya.

Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben na Yagba, ta na mai tabbatar da cewa APC ce ta yi nasara da kuri’u 350. ‘Dan takarar jam’iyyar Wada Musa ya zo na biyu ne a zaben da kuri’u 62.

KU KARANTA: Dino Melaye ya ce an kashe wani 'Danuwansa wajen zaben 2019

Jami’in hukumar zaben, Dr. Okor Henry, shi ne ya bada wannan sanarwa. Haka zalika Malamin zaben ya bayyana cewa ‘Dan takarar Sanatan APC ya samu kuri’a 480 yayin da PDP ta samu 53.

Wada Musa wanda ya tsayawa jam’iyyar PDP a zaben gwamnan ya samu kuri’a 1, 109 a Mazabar Kakanda da ke Birnin Lokoja. INEC ta ce Yahaya Bello na APC ya yi galaba da kuri’u 5, 631.

Jam’iyyar PDP ba ta iya kai labari a cikin karamar hukumar Kabba-Bunu ba inda ta zo na biyu bayan APC. Yahaya Bello ya samu kuri’a 15, 364, ya sha gaban Wada Musa mai kuri’u 8084.

Kola Ologbondiyan wanda shi ne Mai magana da yawun bakin jam’iyyar PDP a Najeriya ya fito daga wannan yanki na Kabba-Bunu ne amma ya gaza karbowa jam’iyyarsa ta PDP Mazabar ta sa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel