Dino Melaye ya sha kaye a kananan hukumomi 4 cikin 6 kamar yadda INEC ta sanar

Dino Melaye ya sha kaye a kananan hukumomi 4 cikin 6 kamar yadda INEC ta sanar

A sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta sanar na kujerar sanatan Kogi na yamma, har yanzu dai Smart Adeyemi na jam'iyyar APC ke gaba inda Dino Melaye na jam'iyyar PDP ke biye.

A cikin kananan hukumomi bakwai da akayi zaben kujerar sanatan, biyar daga ciki an bayyana sakamakonsu

A cikin kananan hukumomin biyar kuwa, Adeyemi na da jimillar kuri'u 60,330 inda Melaye ke biye dashi da jimillar kuri'u 46,836.

Adeyemi ya lashe zaben a kananan hukumomin Kabba Bunu, Kogi Koton Karfe, Mopa Muro da Ijumu. Melaye kuwa ya samu lashe karamar hukumar Yagba ta gabas ne.

Dukkannin 'yan takarar kujerar sanatan daga karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogin suke.

DUBA WANNAN: Dino Melaye ya sha mugun kaye a karamar hukumarsa

Kamar yadda nasara a halin yanzu ta ke hannun Adeyemi, akwai bukatar Melaye ya cike gibin kuri'u 13,494 daga sauran kananan hukumomi biyu, kamar yadda sakamakon INEC ya nuna.

Wadannan kananan hukumomin kuwa su ne: Yagba ta yamma da karamar hukumar Lokoja.

Ga sakamakon kananan hukumomi biyar cikin bakwai din da hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar.

Karamar hukumar Kabba Bunnu

APC — 15,037

PDP — 8,974

Karamar hukumar Kogi Koton Karfe

APC — 14,168

PDP — 9,786

karamar hukumar Mopa Muro

APC — 4,874

PDP — 3,704

Karamar hukumar Ijumu

APC — 11,627

PDP — 7,647

Karamar hukumar Yagba ta gabasa

APC — 6,683

PDP — 7,745

Karamar hukumar Yagba ta yamma

APC 7, 941

PDP 8, 980

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel