APC ta na gaba a kuri’un da aka soma tattarawa a Gabashin Bayelsa

APC ta na gaba a kuri’un da aka soma tattarawa a Gabashin Bayelsa

‘Dan takarar jam’iyyar APC mai adawa a jihar Bayelsa, David Lyon, ya na iya karbe mulkin jihar daga hannun PDP bayan sakamako sun fara nuna cewa ya na kan gaba a zaben Ranar Asabar.

Sakamakon zaben sabon gwamnan da aka yi Ranar 16 ga Nuwamba ya bayyana cewa David Lyon na jam’iyyar APC ya yi galaba a kan ‘dan takarar PDP a wasu rumfunan Ogbia da kuma Nembe.

Kamar yadda mu ka samu labari, sakamakon zaben da su ke fitowa sun nuna cewa jam’iyyar APC ce ta ke kan gaba a wadannan manyan Garuruwa na gabashin jihar Bayelsa a zaben na 2019.

A wani akwati da ke Mazabar Nembe a Garin Ogbolomabiri, jam’iyyar APC mai hamayya ta samu kuri’a 67 inda ta ribanya PDP fiye da sau uku a akwatin wanda ta za na biyu da kuri’u 20.

KU KARANTA: Gwamna ya nemi a soke zaben Bayelsa saboda magudin APC

A wani rumfan da ke Ogbolomabiri, APC ta samu kuri’u 112. Jam’iyyar PDP ba ta iya samun ko da kuri’a daya a akwatin ba. Jam’iyyar Accord, LP, da AD sun samu kuri’a bakwai gaba dayansu.

A rumfa na biyu a Garin Ogbolomabiri, APC ta na da kuri’a 111, PDP ta samu uku. A rumfa na 14 kuma, APC ta samu 492, PDP ta tashi da 29. A rumfa na 9 an ba PDP ratar kuri’a fiye da 160.

Har ila yau a Gundumar Kolo da ke cikin yankin Mazabar Ogbia, APC ta samu kuri’u 1, 200, yayin da PDP mai rike da jihar ta kare a ta biyu da kuri’u 923 kamar yadda sakamako su ka fita.

A cikin Unguwar Agudama-Epie da ke babban birni Yenagoa, akwai akwatin da APC ta samu kuri’a 780, PDP kuma ta samu 54. Hakan ya nuna nasarar APC har a cikin shiyyar tsakiyar jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel