‘Danuwana da aka harbe a filin zabe ya mutu – Inji Dino Melaye

‘Danuwana da aka harbe a filin zabe ya mutu – Inji Dino Melaye

‘Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya bayyana cewa ya rasa wani ‘Danuwansa a zaben maiman kujerar ‘Dan majalisan da gwamna da ake yi.

Sanatan jam’iyyar hamayyar ya fito shafinsa na Tuwita ne ya na ikirarin cewa ‘Dan ‘yanuwansa da aka harbe a Ranar Asabar, 16 ga Watan Nuwamba, 2019, ya riga mu gidan gaskiya.

Dino Melaye da ke kokarin kare kujerarsa a majalisar dattawan Najeriya a zaben da ake yi, ya ce Mista Olorunjuwon da ake harbe jiya Asabar ya mutu a safiyar yau Ranar Lahadin nan.

Dino ya yi wannan bayani ne a dandalin sadarwa na Tuwita ya na mai cewa: “’Danuwana Olorunjuwon da aka harbe a rumfar zabe na jiya (Asabar), ya mutu yau da safen nan (Lahadi).”

KU KARANTA: Dino Melaye dumu-dumu a hotuna ya na sabawa dokar zabe a Kogi

Jawabin ‘dan majalisar tarayyan mai wakiltar Yammacin Kogi ya kara da cewa: “’Danuwana, mutuwa ce kolo-luwar sadaukar da kan da ka yi domin ceto mutanen al’ummar mu.”

Idan ba ku manta ba, a jiya, an samu wasu ‘yan bangar siyasa da su ka dura rumfar zaben Sanatan a motoci biyu inda su ka yi watsa-watsa da kayan zabe bayan sun harbe bindiga a iska.

Kafin nan dai ‘Dan majalisar ya yi ta wallafa wasu sakamakon zabe da hukumar INEC ba ta tabbatar da su ba. Daga baya kuma ya fito ya na kukan cewa ana yunkurin murde zaben.

Bayan Sanatan dai babu wanda ya iya tabbatar da rasuwar wannan Bawan Allah. Dino Melaye ya kuma nuna wasu hotunan bizne wani da ake zargin ‘Yan daban APC ne su ka kashe shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel