Dino Melaye ya sha mugun kaye a karamar hukumarsa

Dino Melaye ya sha mugun kaye a karamar hukumarsa

Dan takarar kujerar sanata na yankin jihar Kogi ta yamma a karkashin jam'iyyar APC, Smart Adeyemi, ya yi nasara akan Dino Melaye na jam'iyyar PDP a karamar hukumar ijumu da ke jihar Kogi.

Dukkan 'yan takarar 'yan asalin karamar hukuma daya ne a jihar Kogi.

Smart Adeyemi dan asalin kauyen Iyara ne inda Dino Melaye kuma dan asalin kauyen Aiyetoro ne da ke da makwabtaka da Iyara.

An sanar da sakamakon zaben karamar hukumar ne a safiyar Lahadi.

Smart Adeyemi na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 11,627, yayin da Melaye na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 7,647 a karamar hukumar. Wannan sakamakon ya fito ne daga hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.

DUBA WANNAN: An bawa masu zabe, ma'aikatan INEC da jami'an tsaro cin hancin N5000, N15000 da N50,000 - YIAGA

Natasha Akpoti ta jam'iyyar SDP ce ke biye da Melaye da tazarar kuri'u 49.

Ijumu wani bangare ce ta yankin jihar Kogi ta yamma, yankin da duk 'yan takarar ke da rajin wakilta.

Jaridar Premium Times ta ruwaito yadda zaben Ijumu ke cike da hargitsi tare da rashin lumana. An samu 'yan daba da suka dinga harbe-harbe tare da fatattakar ma'aikatan wucin-gadi na INEC da masu lura da zabe. A kalla mutum daya ne ya samu raunika daga harbe-harben bindigar da 'yan dabar suka yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel