Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar tseratar da mata da kananan yara daga 'yan Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar tseratar da mata da kananan yara daga 'yan Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar tseratar da mata da kananan yara daga hannun 'yan ta'addan Boko Haram a karamar hukumar Gwoza da ke jihar Barno.

Kamar yadda mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Aminu Iliyasu ya sanar a ranar Lahadi, an tseratar da mutanen ne bayan da aka fi karfin mayakan Boko Haram din a karamar hukumar Gwoza a ranar Asabar. Wadanda aka tseratar din sun hada da mata hudu da kananan yara hudu.

Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar tseratar da mata da kananan yara daga 'yan Boko Haram
Sojin Najeriya tare da mata da yaran da suka tseratar
Source: Twitter

Kanal Iliyasu yace, kungiyar ma'aikatan lafiya ta rundunar sojin sun hanzarta yi wa yaran rigakafin cutar shan inna. An samo wata tsohuwa mai shekaru 80 a duniya a cikin wadanda 'yan ta'addan suka yi garkuwa dasu. Amma ba a tabbatar ko tana bukatar tallafin ma'aikatan lafiya da gaggawa ba.

Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar tseratar da mata da kananan yara daga 'yan Boko Haram
Tsohuwa mai shekaru 80 da sojin Najeriya suka tseratar
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An bawa masu zabe, ma'aikatan INEC da jami'an tsaro cin hancin N5000, N15000 da N50,000 - YIAGA

A samamen da sojin suka kai, ba a samu wadanda suka halaka ba ko suka samu rauni ta bangaren sojin, in ji Iliyasu. Wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne sun tsere zuwa cikin tsaunikan Mandara tare da munanan raunikan da suka samu daga harbin bindiga.

"Jajircewa da kokari irin na rundunar sojin abun jinjinawa ne. Zamu cigaba da kokari wajen ganin mun raba garin mai cike da tsaunika da 'yan ta'addan," in ji shi.

Tuni dai wadanda aka ceto din suka shiga jerin sauran 'yan Najeriyar da aka kwato daga hannun 'yan ta'addar a cikin shekarun nan. 'Yan ta'addan kan sace mutane lokuta da dama don su horar dasu a matsayin mayakansu, bayinsu ko saboda kudin fansa.

Mai magana da yawun rundunar sojin ya ce, zasu cigaba da amfani da sahihan bayanan sirri a kan maboyar 'yan ta'addan a fadin yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel