Zaben Bayelsa: Seriake Dickson ya bukaci INEC ta rusa zaben Nembe da Kudancin Ijaw

Zaben Bayelsa: Seriake Dickson ya bukaci INEC ta rusa zaben Nembe da Kudancin Ijaw

Gwamna Seriake Dickson na jihar Bayelsa ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta watau INEC ta soke duk zabukan da aka yi a wuraren da rikici ya barke sannan kuma aka sabawa ka’idoji.

Mai girma Seriake Dickson ya nemi hukumar INEC ta rusa sakamakon zaben karamar hkumar Nembe. ‘Dan takarar gwamnan APC, Mista David Lyon ya fito ne daga wannnan Gari na Nembe.

Idan ba ku manta ba, David Lyon, ya samu kuri’a 1000 ne a akwatin zabensa yayin da jam’iyyar PDP mai rike da mulki da ‘dan takararta watau Sanata Douye Diri ta samu kuri’u 22 a rumfar.

Gwamna Dickson mai shirin barin-gado ya bayyana cewa an yi murdiya a wannan Gari, ya ce: “’Yan kwangilar mai; Gabriel Jonah da wani Kodjo Sam sun dauko hayar ‘yan daba a zaben.”

Mai girma gwamnan ya kara da cewa: “Ina kira ga shugaban hukumar INEC ya bada umarni a soke zabe a duka gunduma da mazabu na kaf kananan hukumomin da wannan abu ya shafa.”

KU KARANTA: Ana murde zabe yanzu haka a ofishin hukumar INEC a Kogi - Dino Melaye

Gwamna Dickson ya bayyana cewa ya na so ne a kashe zaben “Duk wurin da aka dauke ko sace kayan zabe, ko aka boye Malaman zabe domin a ba jam’iyyar APC damar tattaro kuri’un karya.”

Dickson ya zargi gwamnatin APC mai mulki a Najeriya da yunkurin kakaba jam’iyya daya a Najeriya. A cewar gwamnan na Bayelsa, an yi amfani da jami’an tsaro wejen taya APC magudi.

Bata-garin Sojoji sun hada-kai da ‘yan daban jam’iyyar APC sun yi murdiya a wasu bangarorin Kudancin Ijaw, Ekeremor da Ogbia kuma babban birni na Yenagoa, inda aka sace kayan zabe.

Kusan kowa ya san babu yadda za ayi APC ta ci zabe a Bayelsa. Amma ta na da Sojoji da ‘yan kwangilar mai da za su iya komai. Gwamnan ya yi kira ga Buhari da IGP su tashi, su dauki mataki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel