An tursasawa Ma’aikatan zabe sa hannu a sakamakon kuri’un bogi a Kogi - Melaye

An tursasawa Ma’aikatan zabe sa hannu a sakamakon kuri’un bogi a Kogi - Melaye

Mun samu labari cewa Dino Melaye ya fito ya fara kokawa da yadda zaben Kogi ya ke gudana inda ya ke ikirarin ana yunkurin murde zaben jihar dare daya ta hanyar amfani da jami’an zabe.

Dino Melaye wanda a Ranar Asabar ya ke ta faman da’awar jam’iyyar hamayya ta PDP ta na kan gaba a wasu rumfunan mazabarsa, ya dawo ya na mai cewa ana tafka magudi a halin yanzu.

‘Dan majalisar wanda ake sake maimaita zabensa ya bayyana wannan ne a shafinsa na dandalin Tuwita a Ranar Lahadi, 17 ga Watan Nuwamba, da kimanin 1:46 zuwa karfe 2:00 na tsakar dare.

Sanatan na Kogi ta yamma ya ke cewa:

“An tursasawa Malaman zabe masu bautar kasa sa hannu a kan sakamakon bogi. Wannan danyen aiki ido rufe. Da Ubangiji kadai na dogara.”

Kafin nan kuma Sanatan ya rubuta cewa:

“Ana canza alkaluma a wajen tattara sakamakon kananan hukumomi. Malaman zabe sun yi wasa da aikinsu.”

KU KARANTA: An ga Dino Melaye dumu-dumu ya na sayen kuri'un Jama'a

Da karfe 1:46 na dare ne Sanatan mai-ci ya jefa babban zargi kan wasu kusoshin gwamnatin jihar ya na mai cewa:

“Ana murde zabe yanzu haka a ofishin hukumar INEC da ke Garin Kabba. Kakakin majalisa Kola (Mathew Prince), Taofik (Kantoma Taofik Isah) da Kwamishinan harkar gona duk su na cikin ofishin INEC.”

Fitaccen Sanatan ya kara da cewa:

“An cusa sakamakon zaben Egbeda da Oke Ofin. An soke sakamakon zaben Mazabar Oke Koko inda PDP ta yi galaba da fiye da kuri’a 1000. Haka zalika an kuma soke zaben Mazabar Odolu.”

Sai dai kawo yanzu da mu ke tattara labarin, jami’an hukumar INEC da bangaren gwamnatin APC a jihar Kogi ba su yi magana a kan wannan zargi masu nauyi da Sanatan ya fito ya na yi ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel