Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta tabbatar da cewa ma’akatanta 30 sun yi dabo a zaben da ake yi a jihar Kogi inda ake gwabzawa tsakanin musamman PDP da kuma jam’iyyar APC.
Wadannan ma’aikata sun yi wa hukumar INEC aikin wucin-gadi ne a Garin Olamaboro. Sai dai har yanzu babu labarinsu kamar yadda hukumar zaben ta bayyana lokacin da aka fara tara kuri’u.
Karamar hukumar Olamaboro nan ne inda ‘dan takarar mataimakin gwamnan na APC watau Edward Onoja ya fito. Jam'iyyar APC sun kuma samu nasara a mazabar Mista Edward Onoja.
Daga cikin wadanda ba a gani ba akwai malaman zabe na PO da APO da su ka yi aiki a rumfunan da ke gundumar Imane a Garin Olamaboro. Wasu ma’aikatan wucin-gadin, masu bautar kasa ne.
Da kimanin karfe 1:00 na dare, jami’an INEC da ya ke sanar da sakamakon kananan hukumomin jihar, Garba Mahmood, ya bayyana cewa ba su da labarin inda ma’aikatan zaben su ka shiga.
Malam Garba Mahmood ya kara da cewa ba a sake jin duriyar malaman zaben ba tun karfe 2:00 na rana, jim kadan bayan mutane sun kammala kada kuri’arsu a mazabun jihar da su ka yi aiki.
A cikin safiyar yau Lahadi, 17 ga Watan Nuwamban 2019, ta tabbatar da cewa ta gaza samun jami’an na ta har a lambobin wayoyinsu. Jami’an tsaro dai ba su iya cewa komai ba kan lamarin.
KU KARANTA: Yadda zaben Kogi ya ke gudana a halin yanzu - Kai tsaye
Ga dai sunayen jami’an da su ka bace da hukuma da jami’an tsaron su ka bada
Mazabar Olamaboro na III
Akwati na 02
Oladipo Victor
Achimi Samson
Umar Faruk Sani
Adama Ibrahim
Akwati na 06
Abayomi Roseline E.
Onojah Emmanuel
Umoru Mariam
Akwati na 13
Effiong Akwaowo-Ukpe
Mattew Agada
Samuel Ibrahim
Sado Bello
Mazabar Imane na 1
Akwati na 06
Nzeofia Kingsley
Hassan Musa
Ekele Michael
Ahmed Mattew
Akwati na 12
Ovioawho Omonefe B
Baba Eric
Gabriel Samuel
Akwati na 15
Nwafor Emmanuel
Agada Ochegeugwa
Ojih Martina
Akwati na 16
Ezugwu Stanley
Mohammed Abdullahi
Mohammed Ibrahim
Adejoh Joy
Akwati na 22
Adebisi Comfort
Yusuf Sofiat
Onoja Alice
Onuche Vincent

Sunayen Jami’an Hukumar INEC da su ka bace wajen zabe
Source: Twitter

Sunayen wasu Jami’an INEC da su ka bace wajen aikin zaben Kogi
Source: Facebook
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan