Zaben Bayelsa: Jama'ar mazabar Jonathan sun yi bikin murnar faduwar PDP

Zaben Bayelsa: Jama'ar mazabar Jonathan sun yi bikin murnar faduwar PDP

- Jam'iyyar APC ta samu nasarar lashe zabe a dukkan akwatuna 13 da ke mazaba ta 9 a karamar hukumar Ogbia, kamar yadda wakilan INEC suka sanar

- Jama'a a mazabar, wacce ta kasance ta tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, sun yi tururuwar fito wa domin nuna faracikinsu

- Legit.ng Hausa tana kawo rahoton kai tsaye a kan zaben jihar Bayelsa da na jihar Kogi

Jama'a a mazaba ta 9, mazabar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, da ke yankin Kolo a karamar hukumar Ogbia, sun yi tururuwar fitowa kan titi domin nuna farincikinsu da faduwar PDP a mazabarsu, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

The Nation ta rawaito cewa jam'iyyar APC ta lashe zabe a dukkan akwatu 13 da ke mazabar, kamar yadda wakilan INEC suka bayyana bayan sun kammala kidayar kuri'un masu zabe.

Wasu daga cikin murnar na dauke da tutar jam'iyyar APC, kamar yadda aka gansu a kan titin garin Ogbia. Wasu daga cikinsu na share kan tititi da tsintsiya tare da bayyana cewa sun sha wahala a hannun gwamnatin PDP mai ci.

Idan zamu tuna, tun a shekarar 1999 da aka fara mulkin damokaradiyya a Najeriya, jihar Bayelsa na daga jihohin da jam'iyyar PDP ke mulka har zuwa yau.

Ganin sakamakon da ke fita, akwai yuwuwar akalar siyasar jihar Bayelsa ta canza.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel