An bawa masu zabe, ma'aikatan INEC da jami'an tsaro cin hancin N5000, N15000 da N50,000 - YIAGA

An bawa masu zabe, ma'aikatan INEC da jami'an tsaro cin hancin N5000, N15000 da N50,000 - YIAGA

- Wata kungiyar matasa mai fafutukar cigaban Afirka (YIAGA AFRICA) ta bayyana abubuwan da suka yawaita a zaben Kogi

- Kungiyar ta ce akwai yawaitar tashin hankali da sayen kuri'a zaben gwamnan jihar Kogin da aka kammala ranar Asabar

- Hakan na kunshe ne wani rahoton 'somin tabi' na sakamakon yadda zaben gwamnan ya gudana a jihar Kogi

Wata kungiyar matasa mai fafutikar cigaban Afrika (YIAGA AFRICA) ta bayyana cewar an samu yawaitar tashin hankali da sayen kuri'a a zaben gwamnan jihar Kogi da aka kammala ranar Asabar.

Hakan na kunshe ne a cikin wani rahoton 'somin tabi' na sakamakon sa idon yadda zaben gwamna ya gudana a jihar Kogi mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar YIAGA AFRICA, Dakta Hussaini Abdu, da darektan sa ido a zaben Kogi, Samson Itodo.

Shugabannin kungiyar sun ce sun baza wakilansu 500 a wasu mazabu 250 da suka zaba daga a kananan hukumar jihar Kogi 21.

"Tunda misalin karfe 12:00 na rana, kungiyar YIAGA AFRICA ta samu rahotanni da suka tabbatar mata da cewa ana bawa masu zabe N5,000 domin sayen kuri'unsu. A mazabar Iyano da ke karamar hukumar Ibaji, mun samu rahoton an bawa ma'aikatan INEC cin hancin N15,000, su kuma jami'an tsaro an basu N50,000 domin su bayar da hadin kai a tafka magudi," a cewar rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel