Sakamakon farko-farko: APC na shirin bawa PDP mamaki a jihar Bayelsa

Sakamakon farko-farko: APC na shirin bawa PDP mamaki a jihar Bayelsa

- Sakamakon da ya karade jihar Bayelsa na nuna akwai yuwuwar samun sauyin akalar siyasar jihar

- A sakamakon da suka bayyana, jam'iyyar APC ce ke kan gaba duk da kuwa PDP ke mulkin jihar tun 1999

- Sakamakon na nuna cewa, dan takarar APC, David Lyon ke lallasa abokin karawarsa na jam'iyyar PDP, Duoye Diri

Gama garin sakamakon zabe da ke fitowa daga jihar Bayelsa na nuni da cewa za a iya samun sauyi a jihar, saboda jam'iyyar APC ce a gaba kamar yadda wasu sakamakon zabe daga Yanagoa, babban birnin jihar Bayelsa suka nuna.

Jam'iyyar PDP ce ke mulkin jihar Bayelsa tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya a shekarar 1999. Masana siyasa na ganin cewa za iya samun canji a jihar saboda canjin shekar da wasu jiga-jigan 'ya'yan PDP suka yi zuwa APC gabanin zaben gwamnan jihar da aka kammala a ranar Asabar.

Sakamakon farko-farkon ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar APC, David Lyon, shine ke lallasa abokin karawarsa, Duoye Diri, dan takarar jam'iyyar PDP.

Ga wasu daga cikin sakamakon da suka fito daga Yenagoa;

Atissa ward 1, unit 9, Yenagoa LGA

PDP – 77 APC – 94

Ikibiri unit 2, Yenagoa LGA

PDP – 51 APC – 108

Agudama-Epie, ward 4, unit 12, Yenagoa LGS

PDP- 24 APC – 368

Agudama-Epie unit 9, Yenagoa LGA

PDP -54 APC – 789

Igbogene-Epie, unit 4, Yenagoa

PDP – 74 APC – 649

Azikoro unit 3, Yenagoa LGA

PDP- 189 APC- 244

Azikoro unit 4, Yenagoa LGA

PDP- 120 APC – 169

Azikoro unit 5, Yenagoa

PDP- 134 APC- 204

Ikibiri, unit 1, Yenagoa

PDP- 64 APC- 256

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel