Daga karshe: Buhari ya warware sarkakiyar sallamar hadiman Osinbajo 35

Daga karshe: Buhari ya warware sarkakiyar sallamar hadiman Osinbajo 35

- Shugaba Buhari ya yi bayanin cewa, umarnin canzawa hadiman Osinbajo ma'aikata kadai ya bayar

- Buhari ya ce, ya bayar da umarnin a mayar da su sabuwar ma'aikatar walwala da jinkai na kasa ne

- Tuni fadar shugaban kasar ta musanta wata baraka tsakanin shugaban kasar da mataimakinsa

A karo na farko, Shugaban kasa Buhari ya yi magana a kan zarginsa da ake da fatattakar hadimai 35 na mataimakinsa.

A yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikiwe dake Abuja, bayan saukarsa daga Landan a ranar Juma'a, 15 ga watan Nuwamba, shugaban kasar ya ce, abin haushi ne da aka fassara umarninsa da 'kora'.

Shugaban kasa Buhari a tattaunawarsa da NTA, ya yi bayanin cewa, bai sallami hadimai 35 na ofishin mataimakinsa ba. A maimakon hakan, an mayar da su wata ma'aikatar ne

Ya kara da cewa, an kirkiro sabuwar ma'aikatar walwala da jin kan 'yan kasa.

DUBA WANNAN: Tirkashi: An kama Dino Melaye yana siyan kuri'u (Hoto)

"Sun ce an sallami hadimai 35 daga ofishin mataimakin shugaban kasa amma an kirkiro ma'aikatar walwala da jin kan 'yan kasa. Wannan ma'aikatar aka turasu. Mutane na fassara abun ta fuskar siyasa da kabilanci. Abun babu dadi," in ji shugaban kasa.

Buhari ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa, ya dawo da karfinsa na yin aiki. Ya yi alkawarin aiki tukuru ta yadda zai nunawa 'yan Najeriya dalilinsa na yanke wasu hukunci.

Akwai rade-radin cewa, akwai baraka fa kasan kasa da ke tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo. Fadar shugaban kasan ta musanta a karo da yawa a kan barakar da ke tsakaninsu.

Ikirarin barakar kuwa ya karu ne bayan da aka sallami hadiman mataimakin shugaban kasar 35 daga

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel