Ma'aikatan INEC sun tsere daga wurin zabe bayan sun sha bugu a hannun 'yan daba

Ma'aikatan INEC sun tsere daga wurin zabe bayan sun sha bugu a hannun 'yan daba

- Jami'an hukumar INEC sun yi ta kansu bayan da suka sha jibga daga wadanda ake zargin 'yan daba ne

- Hakan ta faru ne a akwati mai lamba 001 na gundumar Asuta da ke karamar hukumar Kabba /Bunu a jihar Kogi

- An yi wa manema labarai da jami'an wucin-gadi na INEC barazana tare da fatattakarsu

Jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC sun tsere tare da barin akwati mai lamba 001 a gundumar Asuta da ke karamar hukumar Kabba/Bunu ta jihar Lokoja bayan da suka sha mugun duka daga wadanda ake zargin ‘yan daba ne.

Jaridar The Cable ta samo wannan rahoton ne wajen karfe 2 na yamma, kafin fara kirga kuri’u.

An samu rahoton lalata kuri’u a akwatuna da dama da ke kananan hukumomin Kabba/Bunu tare da Ijumu na jihar Kogi.

DUBA WANNAN: Tirkashi: An kama Dino Melaye yana siyan kuri'u (Hoto)

A akwati mai lamba 006 na gundumar Asuta da ke karamar hukumar Kabba/Bunu, an fara kirga kuri’u inda jam’iyyar PDP ke jagoranta da kuri’u mafiya rinjaye lokacin da wasu matasa suka watsa wa kuri’un ruwa.

An yi wa manema labarai da jami’an wucin-gadi na INEC barazana tare da fatattakarsu.

Zaben ya zo ne da rashin zaman lafiya tare da hargitsi ballantana a jihar Kogi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel