Wani kwale-kwale dauke da yan jarida a garin Sampou, karamar hukumar Kolokuma Opokuma ta jihar Bayelsa ya kife cikin rafi.
Yan jaridan sun shiga ne domin samo labarai kan yadda abubuwa ke wakana a zaben yau.
Bayan kammala dauko rahoton zabe inda suka je, suna hanyar dawowa ne kwale-kwalen ya zubar da su cikin rafi amma wasu yan gari suka tsamosu cikin ruwa.
Wayoyi, kamara da kayan aikinsu duk sun nutse.
An yi ambaliya a unguwar da rumfar zaben dan takaran jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Sen. Douye Diri, ya kada kuri'arsa, shi yasa yan jaridan suka shiga kwale-kwale.
Ambaliyan ya janyo jinkiri sosai kafin aka kaddamar da zabe misalin karfe 10 na safe.
KARANTA: KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihar Bayelsa (Hotuna)
Wuraren da irin wannan ambaliya ya shafa sun hada da, Amasoma, Yenagoa da Sagbama.
A bangare guda, Hukumar Zabe mai zaman kanta na kasa (INEC) bayyana dalilin da yasa aka samu jinkirin fara zabe a rumfar zaben tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan dake jihar Bayelsa.
INEC ta ce 'yan daba da suka kai wa ma'aikatan ta hari a karamar hukumar Ogbia ne suka yi dalilin jinkirin.
Hukumar ta ce wannan shine dalilin da yasa aka samu jinkirin awanni uku kafin aka fara jefa kuri'a a akwatin zaben tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng