Yanzu Yanzu: Wada ya kada kuri’a, ya zargi yan daban APC da yunkurin kwace akwatunan zabe

Yanzu Yanzu: Wada ya kada kuri’a, ya zargi yan daban APC da yunkurin kwace akwatunan zabe

- Wada na jam’iyyar PDP ya kada kuri’a a zaben gwamna da ke gudana

- Dan takarar gwamnan ya zargi yan daban APC da kwace akwatunan zabe

- A cewarsa yan daban APC basu san komai ba sama da kwace akwatunan zabe

Wasu yan iska da ake zargi da yiwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki aiki sun yi kokarin tarwatsa zabe a jihar Kogi.

Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Musa Wada ne ya yi zargin.

Ya yi zargin cewa yan iskan sun yi kokarin tarwatsa zabe a mazabarsa amma matasan garin da jami’an tsaro suka dakile harin.

A cewarsa, yan iskan na APC ba su san komai ba sama da kwace akwatunan zabe da dangwala kuri’u.

Wada wanda ya bayyana hakan ya jaridar Premium Times bayan kada kuri’arsa a kauyensa ya Odu Ogboyaga, a rumfar zabe ya 001, unguwa 4, ya ce yana fatan shine zai yi nasara.

Dan takarar wanda ya ce ya yi wuri da yawa yanke hukunci kan ko anyi zabe na gaskiya ya yaba ma jami’an tsaro akan wanzar da zaman lafiya zuwa yanzu.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: An kama Dino Melaye yana siyan kuri'u (Hoto)

Wada ya kuma bayyana cewa an samu labari daga wasu yankuna cewa yan iska na kwace akwatunan zabe.

A baya mun ji cewa wasu 'yan bangan siyasa sun kai farmaki rumfunan zabe sun sace akwatunan zabe dauke da kuri'u a garin Anyigba a karamar hukumar Dekina na jihar Kogi.

Anyingba dai gari ne da ya yi kaurin suna wurin rikici hakan yasa adadin jami'an tsaro da aka tura garin ya dara na sauran garuruwan dake karamar hukumar.

Acewar wata majiya, 'yan daban sun iso rumfar zaben cikin motocci suna ta harbe-harbe da bindiga hakan ya razana masu zabe suka tsere sannan suka yi awon gaba da akwatunan zaben.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel