Yanzu-yanzu: An bindige mutane 2 a jihar Kogi

Yanzu-yanzu: An bindige mutane 2 a jihar Kogi

Yayinda sakamakon zabe suka fara fitowa daga jihar Kogi, an bindige mutane biyu a rumfar zaben ofishin yan sanda dake Egume, karamar hukumar Dekina ta jihar, mahaifar dan takaran jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP.

Waus yan bindiga sanye da rigunan soji ne suka dira unguwar inda suka bindige mutane biyu.

\Masu idanuwan shaida sun bayyana cewa abin ya faru ne yayinda mutane ke cikin kada kuri'unsu kawai sai suka fara jin harbi.

An bayyana sunayen wadanda suka rasa rayukansu a matsayin Umoru Shuaib da Faruk Sulaiman.

Wani mai idon shaida, Micheal Ochimamna ya ce: "Sun zo cikin motar bas yayinda ake zabe sanye da rigunan yan sanda, bamu ankara ba."

"Umoru ya kammala zabensa amma yana hira da Faruk a rumfar zaben, kawai sai motar ta shigo."

Kawai sai mukaji harbin bindiga, kafin mun ankara sun gudu.

A yanzu haka mutane sun kauracewa unguwar.

A wani labarin daban, rahotannin sun bayyana cewa rikici ya barke a rumfunan zabe akalla hudu a Lokoja, babbar birnin jihar.

Wasu 'yan bangan siyasa sun kai farmaki rumfunan zabe sun sace akwatunan zabe dauke da kuri'u a garin Anyigba a karamar hukumar Dekina na jihar Kogi.

Anyingba dai gari ne da ya yi kaurin suna wurin rikici hakan yasa adadin jami'an tsaro da aka tura garin ya dara na sauran garuruwan dake karamar hukumar.

A rumfa mai lamba 001 da 006, Asuta, Kabba/Bunu, jam'iyyar PDP na kan gaba yayinda aka fara kirga kuri'u amma wasu yan baranda suka fara watsa ruwa cikin akwati kuma aka fitittiki yan jarida da jami'an INEC

Source: Legit

Tags:
Online view pixel