Zaratan Sojojin Najeriya sun mayar da biki a kan mayakan Boko Haram a Borno

Zaratan Sojojin Najeriya sun mayar da biki a kan mayakan Boko Haram a Borno

Dakarun rundunar Sojojin Najeriya sun kaddamar da wani samame a kan mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram a kauyen Malam Fatori dake cikin karamar hukumar Abadam na jahar Borno, inda suka kashe yan ta’adda da dama.

Kaakakin jami’I mai kula da sashin watsa labaru na rundunar Sojan kasa, Kanal Aminu Iliyasu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Asabar, inda yace yan ta’addan sun yi kokarin kai ma Sojoji harin ramuwar gayya ne biyo bayan nasarar da Sojoji suka samu a kansu a ranar Laraba.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta sha suka: Ki fara gafarta ma Mamman Daura kafin ki nema ma gwamnan Kogi gafara

Aminu yace yan Boko Haram sun kaddamar da harin ne da sanyin safiyar Juma’a, amma suka yi rashin sa’a sakamakon Sojojin Najeriya na zaune cikin shirin ko-ta-kwana, don haka koda suka yi kokarin kutsa kai cikin sansanin Sojojin, sai Sojoji suka mayar da wuta.

“A cikin hanzari tare da nuna kwarewa Sojojin Najeriya suka murkushe mayakan ta’addanci, inda suka kona wata motar yaki da yan ta’addan kurmus tare da yan Boko Haram uku dake cikin motar. Haka zalika mun kashe wasu yan ta’addan guda biyu.

“Sa’annan jiragen yaki na dakarun rundunar Sojan sama sun yi ma sauran yan ta’addan da suka tsere suka yi musu ruwan wuta. Daga cikin makaman da muka kwato akwai samfurin bindigu daban daban, alburusai da dama.” Inji shi.

Sai dai sanawar ta bayyana cewa dakarun Sojin Najeriya guda biyu sun samu rauni, wanda tuni aka garzaya dasu zuwa asibitin Sojoji domin samun kulawar da ta dace, kuma a yanzu haka sun farfado.

Daga karshe, sanarwar ta kara da cewa babban kwamandan Operation Lafiya Dole Manjo Janar Olusegun Adeniyi ya jinjina ma Sojojin bisa jarumtar da suka nuna, a madadin babban hafsan sojan kasa,Laftanar Janar Buratai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel