Mataimakin gwamnan Legas ya jefa matafiya cikin rudani a cikin jirgin sama

Mataimakin gwamnan Legas ya jefa matafiya cikin rudani a cikin jirgin sama

Matafiya a cikin jirgin sama sun shiga cikin halin rudani yayin da suka ci karo da mataimakin gwamnan jahar Legas, Obafemi Hamzat a cikin wani jirgin sama da ya tashi daga jahar Legas zuwa babban birnin tarayya Abuja.

Jaridar The Nation ta ruwaito Hamzat na kan hanyarsa ta zuwa babban birnin tarayya Abuja ne domin halartar wani muhimmin taro, sai dai koda aka tuntubi kamfanonin jiragen sama dake zuwa Legas, sai ba’a samu tikitin masu daraja ba, watau First Class.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta sha suka: Ki fara gafarta ma Mamman Daura kafin ki nema ma gwamnan Kogi gafara

Sai dai a rashin wannan rukuni na First Class, sai Hamzat ya nemi a bashi tikitin jirgin na gama gari, watau, Economy Class, saboda yana matukar son halartar wannan muhimmin taro a babban birnin tarayya Abuja.

Bayan samun tikitin rukunin matafiya gama gari, sai kwatsam aka hangi Hamzat ya shigo cikin matafiya gama gari, nan fa mutanen dake cikin wannan rukuni suka shiga gunaguni da zare idanu sakamakon ba’a saba ganin gwamna ko mataimakinsa suna shiga wannan rukuni ba.

Abin ka da yan Najeriya, wasu daga cikin matafiyan basu yarda da abinda idanunsu yake gani ba, inda a lokacin da jirgin ya sauka, sai suka tunkari mataimakin gwamnan suna tambayarsa

“Ya mai girma, me ke faruwa ne? shin ba kudi a gwamnatin Legas ne da har zaka dinga hawa Economy? Shin da gaske ne wani mutum ya sace kudaden jahar Legas?”.

Bude bakin Hamzat ke da wuya, wanda ya cika da mamaki tare da murmushi sai yace burinsa shi ne ya samu tikitin yin tafiya domin halartar muhimmin taro, kuma ya yi amfani da kujerar da aka samu.

“Abu mafi muhimmanci shi ne ina son ganin kaina a babban birnin tarayya Abuja, kuma yanzu ina Abuja.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel