Yanzu-yanzu: 'Yan daba sun sace akwatin zabe a Anyigba

Yanzu-yanzu: 'Yan daba sun sace akwatin zabe a Anyigba

Wasu 'yan bangan siyasa sun kai farmaki rumfunan zabe sun sace akwatunan zabe dauke da kuri'u a garin Anyigba a karamar hukumar Dekina na jihar Kogi.

Anyingba dai gari ne da ya yi kaurin suna wurin rikici hakan yasa adadin jami'an tsaro da aka tura garin ya dara na sauran garuruwan dake karamar hukumar.

Acewar wata majiya, 'yan daban sun iso rumfar zaben cikin motocci suna ta harbe-harbe da bindiga hakan ya razana masu zabe suka tsere sannan suka yi awon gaba da akwatunan zaben.

DUBA WANNAN: Tirkashi: An kamo Dino Melaye yana siyan kuri'u (Hoto)

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel