Yanzu-Yanzu: 'Yan daba sun sace akwatunan zabe a rumfar zaben Dino Melaye

Yanzu-Yanzu: 'Yan daba sun sace akwatunan zabe a rumfar zaben Dino Melaye

- Wasu da ake zargin 'yan daba ne suka kai hari a rumfar zaben da Dino Melaye ya kada kuri'arsa

- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan dabar sun yi awon gaba da akwatunan zabe da wasu kayayyakin

Wasu 'yan daba sun sace akwatunan zabe tare da fatattakar masu kada kuri'a a rumfar zabe mai lamba 004, gundumar Ayetoro ta daya da ke karamar hukumar Ijumu da ke jihar Kogi.

Wannan rumfar zabe kuwa, itace wacce Dino Melaye ke kada kuri'a.

Sanata Dino Melaye ya tabbatar da afkuwar lamarin a shafinsa na Twitter amma ya ce lamarin ya faru ne bayan ya bar rumfar zaben.

An ce 'yan daban sun iso wurin zaben ne cikin wata bakar mota kirar Hilux

Melaye ya ce: "Jim kadan bayan na bar rumfar zabe ta, wasu 'yan daba da Falake ke yi wa jagora sun zo suna harbe-harbe sun sace akwatunan zabe."

DUBA WANNAN: Ara: Wani karamin gari a Najeriya da babu kare ko guda

Sai dai a halin yanzu babu cikakken bayani kan afkuwar lamarin duba da cewa Hukumar Zabe mai zaman kanta INEC ko rundunar 'yan sandan Najeriya ba su fitar da sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Idan ba a manta ba dai, an soke nasarar Dino Melaye ne mai wakiltan Kogi ta Yamma bayan dan takarar jam'iyyar APC, Smart Adeyemi ya shigar da kara a kotu na kallubalantar zaben da Melaye ya yi nasara.

Hankulan mutane ya fi karkata kan Melaye da Adeyemi ne duk da cewa akwai wasu 'yan takara 22 dake fafatawa a zaben dake gudana a yau Asabar 16 ga watan Nuwamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel