Yanzu-yanzu: Wakilin SDP ya sha duka yayin da 'yan daba suka tarwatsa zabe a Okehi

Yanzu-yanzu: Wakilin SDP ya sha duka yayin da 'yan daba suka tarwatsa zabe a Okehi

Wani wakilin jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ya sha dukkan tsiya a yayin da wasu 'yan daba suka tarwatsa zabe a Obeiba/Ihima a karamar hukumar Okehi na jihar Kogi.

Yar takarar gwamna na jam'iyyar SDP, Natasha Akpoti ta yi ikirarin cewa ana ta harbe-harben bindiga kamar yadda ta bayyana a shafinta na Facebook.

The Cable ta ruwaito cewa ta gano wani mutum yayin da jami'an tsaro ke saka shi cikin motarsu bayan harbe-harben bindigar ta lafa.

Yanzu-yanzu: Wakilin SDP ya sha duka yayin da 'yan daba suka tarwatsa zabe a Okehi
Hoton agent din jam'iyyar SDP da 'yan daba suka yi wa duka a Kogi
Source: Twitter

DUBA WANNAN: PDP ta yi martani kan durkusawa da El-Rufai ya yi yana rokon al'umma su yi wa Yahaya Bello afuwa

A yanzu dai hankulan mutane ya kwanta bayan da jami'an tsaro suka isa Obeiba/Ihima.

Tuni dai an fara zabe a halin yanzu.

Ku saurari karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel