Daga karshe: DSS ta damke wanda ya kera lambar 'Chip Whip'

Daga karshe: DSS ta damke wanda ya kera lambar 'Chip Whip'

Hukumar kiyaye hadurra da hukumar jami’an tsaron farin kaya sun cafko wadanda suke hada lambobin mota na bogi a jihohin Kano da Kebbi. Daga cikin wadanda aka cafken akwai wadanda suka hada lambar motar ‘Chip Whip’.

Lambar motar da aka danganta da bulaliyar majalisar jihar Kano ta jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta na zamani.

Babban jami’in hukumar kiyaye hadurra, FRSC, Boboye Oyeyemin, ya umarci Zubairu Mato, shuagaban hukumar a jihar Kano, su hada kai da jami’an tsaro don gano wadanda ke hada lambobin motar na bogi a jihar.

DUBA WANNAN: Zaben sanata na Kogi: Melaye, Adeyemi da wasu 'yan takara 22 za su fafata a yau (cikakken sunaye)

Ya ce, jami’an tsaron farin kaya a jihar Kano, tuni suka bazama don binciko masu wannan aiki.

A ranar 12 ga watan Nuwamba ne, jami’an tsaro na fararen kaya suka kai samame Sabon Gari, Kofar Ruwa, Gidan Boss wato Kofar Mazugal, Kofar Wambai (‘Yan Robobi) da Naibawa titin Zaria,” in ji shi.

A Sabon Gari, an cafko wanda ake zargin ne inda daga baya aka mikasa gaban kotu. Lokacin da aka kama wanda ake zargin, yana kokarin haka rami ya boye haramtattun lambobin motar da yake hadawa don ya gujewa kamen.” a cewarsa.

An gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotun majistare a ranar Juma’a a Birnin Kebbi. Duk da sun musanta aikata laifin da ake zarginsu, alkalin ya bukaci da a cigaba da tsaresu har zuwa ranar 28 Nuwamba 2019 inda za a cigaba da sauraron karar,” in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel