Zaben Bayelsa: Jonathan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda zabe ke tafiya

Zaben Bayelsa: Jonathan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda zabe ke tafiya

- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, ya nuna rashin jin dadinsa a kan rashin isowar ma'aikatan zabe da wuri

- Da wuri tsohon shugaban kasar ya fito daga gidansa don kada kuri'a a gunduma ta 13, akwati mai lamba 39 a Otueke

- Tsohon shugaban kasar bai samu damar haka ba saboda babu amo balle labarin ma'aikatan hukumar zaben a wajen

Tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan ya nuna rashin jin dadinsa a kan rashin isowar jami'an zabe gunduma ta 13, akwati na 39 da ke Otueke, karamar hukumar Ogbia, inda zai kada kuri'arsa.

Jonathan, ya fito daga gidansa ne don duba ko ma'aikatan zaben sun hallara yayin da yaci karo da wakilin Legit.ng a wajen zaben.

Ya girgiza kansa cike da rashin jindadi.

DUBA WANNAN: Zaben sanata na Kogi: Melaye, Adeyemi da wasu 'yan takara 22 za su fafata a yau (cikakken sunaye)

Yayin komawa gida, ya yi wasu kalamai masu nuna rashin jindadinsa a kan yadda abubuwa ke tafiya.

"Kai jami'in zabe ne?" Ya tambayi wakilinmu kafin ya kara da "Ina suke?".

"Toh... A nan zan kada kuri'a, amma tunda ba su zo ba har yanzu, bari in koma ciki."

"Ka gani ko, matasa a yanzu yakamata ku kara dagewa," ya kara da cewa yayin taba kafadar wakilinmu yayin da yake komawa cikin gidansa.

Har zuwa karfe 8:19 na safiyar yau, ba a kawo kayayyakin zabe ba a inda yakamata a aje akwatin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel