Aisha Buhari ta sha suka: Ki fara gafarta ma Mamman Daura kafin ki nema ma gwamnan Kogi gafara

Aisha Buhari ta sha suka: Ki fara gafarta ma Mamman Daura kafin ki nema ma gwamnan Kogi gafara

Tsohon hadimin shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya caccaki uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari game da magiyar da ta yi ma jama’an jahar Kogi inda ta nemi su gafarta ma gwamnan jahar, Yahaya Bello.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Omokri ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Twitter, inda yace idan har Aisha na son jama’an Kogi su gafarta ma Yahaya Bello, toh ta fara yafe ma Mamman Daura da iyalansa.

KU KARANTA: Ana zaton wuta a makera: Dansanda ya yi ma diyar Yarsanda fyade a cikin barikin Yansanda

Aisha Buhari ta nemi jama’an jahar Kogi su gafarta ma Yahaya Bello ne biyo bayan rashin biyan albashi da gwamnatinsa ta hana ma’aikata tsawon shekara da shekaru, a yayin da yake neman zarcewa a kan kujerar gwamnan karo na biyu.

Aisha ta tabbatar ma jama’an Kogi cewa Gwamna Yahaya Bello zai biya bashin albashin ma’aikatan saboda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga cikin maganan, kuma ta basu tabbacin ba zai sake basu kunya ba.

Sai dai Reno ya yi bara’a da ra’ayin Aisha, inda yace: “Idan har Aisha na son mutanen Kogi su yafe ma Yahaya Bello, mutumin da ya kwashe shekaru ba tare da biyansu albashi ba, toh ta fara gafarta ma Mamman Daura da iyalansa, sa’annan ta dawo dasu cikin fadar shugaban kasa Aso Rock Villa.”

A wani labarin kuma, Kwamitin tattaunawa tsakanin gwamnatin jahar Legas da kungiyoyin kwadago a jahar sun amince da biyan ma’aikatan jahar jahar karancin albashin N35,000, inda ta yi ma ma’aikata karin N5,000 fiye da na abin da doka ta tanada.

Gwamnan jahar Legas, Babatunde Sanwo Olu ya bayyana aniyarsa ta fara biyan sabon karancin albashin daga watan Nuwamba da muke ciki, inda yace sun yanke wannan shawara ne bayan kammala tsara yadda albashin zai shafi matakai daban daban na aikin gwamnati.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel