An zargi Buhari da burin neman tazarce shi yasa yake kuntata ma yan jaridu

An zargi Buhari da burin neman tazarce shi yasa yake kuntata ma yan jaridu

Fitaccen mai rajin kare hakkin biladama a Najeriya, Femi Falana ya bayyana cewa yadda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kuntata ma yan jaridu manuniya ce ta shirinsa na neman zarcewa a kan mulki karo na uku.

Falana ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da kasida a taron kaddamar da wani littafi mai taken ‘Testimony to courage’ da aka wallafa a kan shugaban kamfanin jaridar Premium Times, Dapo Olorunyomi, a jahar Legas.

KU KARANTA: Ana zaton wuta a makera: Dansanda ya yi ma diyar Yarsanda fyade a cikin barikin Yansanda

Lauya Falana yace: “Najeriya na cikin mawuyacin hali, don haka bai kamata kafafen watsa labaru su yi shiru ba, nan bada jimawa ba watakila ku fara jin an fara kokarin neman tazarce karo na uku. Nan bada jimawa ba zasu fara yaki da yan adawa.

“Amma ko ba zamu bari su lalata kafafen watsa labaru ba, babu wani mai mulkin kama karya daya isa ya danne yan Najeriya.” Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito shi.

Babban lauyan ya bayyana damuwarsa da yadda Alkalin babbar kotun tarayya dake zamanta a Legas, mai shari Ijeoma Ojukwu take gudanar da shari’ar Omoyele Sowore, inda yace bai taba ganin irin sharuddan belin data gindaya masa ba.

“Duk laifin barayin Najeriya basu taba samun irin wannan sharuddan ba, babu wanda ya taba sanya musu takunkumi game da zirga zirgansu, amma sai ga shi an baiwa Sowore beli, amma kuma an cigaba da rikeshi a Abuja, iyalansa kuma na Amurka.

“Ba a Abuja yake zama ba, ba shi da gida a Abuja, amma an umarce shi ya zauna a Abuja. Za iya kwashe shekaru 10 ana shari’ar nan, amma ba zai iya barin Abuja ba, ba’a taba yin haka a Najeriya ba.

"A matsayinsa na dan jarida kotu ta hanashi magana, sa’annan ta hanashi magana taron siyasa a matsayinsa na dan siyasa, har sai ta yanke hukunci, bamu san ranar kammala shariar ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel