Abin ya zama gasa: Ma’aikata za su samu karancin albashin N35,000 a wata jahar kudancin Najeriya

Abin ya zama gasa: Ma’aikata za su samu karancin albashin N35,000 a wata jahar kudancin Najeriya

Kwamitin tattaunawa tsakanin gwamnatin jahar Legas da kungiyoyin kwadago a jahar sun amince da biyan ma’aikatan jahar jahar karancin albashin N35,000, inda ta yi ma ma’aikata karin N5,000 fiye da na abin da doka ta tanada.

Gwamnan jahar Legas, Babatunde Sanwo Olu ya bayyana aniyarsa ta fara biyan sabon karancin albashin daga watan Nuwamba da muke ciki, inda yace sun yanke wannan shawara ne bayan kammala tsara yadda albashin zai shafi matakai daban daban na aikin gwamnati.

KU KARANTA: Ana zaton wuta a makera: Dansanda ya yi ma diyar Yarsanda fyade a cikin barikin Yansanda

A jawabinsa, shugaban kwamitin tattaunawar, Kwamared Rasaq Adio Falade ya bayyana cewa sun cimma yarjejeniya game da karin da kowanne ma’aikaci zai samu a albashinsa duba da matakin da yake kai.

Falade yace ma’aikatan dake mataki na 1 zuwa mataki na 6 zasu samu karin N35,000, ma’aikacin dake mataki na 7 zai samu karin kashi 30 na albashinsa, daga mataki na 8 zuwa na 10 kuwa zasu samu kashi 25 na albashinsu, mataki na 12 – 15 samu samu kashi 22.5 yayin da mataki na 15-17 zasu samu kashi 20.

Shi ma Falade ya tabbatar ma ma’aikata cewa zasu fara gani a miyarsu tun daga albashin watan Nuwamba, sai dai yace game da batun alawus alawus na musaman na malamai, ma’aikatan kiwon lafiya, likitoci da sauransu dake cikin tsarin albashinsu na musamman, na nan yadda yake a dokar 2011.

Daga karshe Falade ya tabbatar da cewa gwamnatin jahar Legas ta yi alkawarin biyan bashin sabon karancin albashin sakamakon tun a watan Afrilu dokar ta fara aiki, don haka zata biya bashin albashin watanni 6 da suka gabata zuwa farkon shekarar 2020.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Fintiri zai fara biyan ma’aikatan gwamnati karancin albashin N32,000, fiye da N30,000 da gwamnatin tarayya ta amince, daga karshen watan Nuwamba da muke ciki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel