Innalillahi: Bidiyon yadda wani sojan Najeriya ya tono jariri sabuwar haihuwa da aka binne da ranshi

Innalillahi: Bidiyon yadda wani sojan Najeriya ya tono jariri sabuwar haihuwa da aka binne da ranshi

- Wani soja da ke aiki da rundunar sojin Najeriya ya fitar da wani bidiyo da ya ja hankulan mutane

- Bidiyon ya nuna yadda aka tseratar da jariri bayan awa bakwai da binneshi

- Mahaifiyar jaririn ce ta binneshi da ranshi saboda ba zata iya daukar nauyin jaririn ba

Wani soja a rundunar sojin Najeriya ya fitar da wani bidiyo mai cike da abun takaici da alhini. Bidiyon dai ya fantsama kafafen sada zumunta na zamani inda yake ta jawo kace nace a wajen jama'a.

A bidiyon kuwa, an nuna yadda wasu suka ceto rayuwar wani jariri wanda aka binne da ranshi a wata jiha dake nan arewacin Najeriya.

Kamar yadda shaidu suka bayyana, mahaifiyar jaririn ce ta binneshi saboda ba zata iya daukar dawainiyarshi ba. Masu wucewa ne suka dinga jin kukan jaririn, Hakan kuwa yasa suka tona ramin, bayan tona ramin mutanen sun tarar da jaririn da ranshi.

KU KARANTA: Kwarto ya yiwa mata da miji dukan tsiya a Kano bayan ya kasa samun biyan bukata

Jaririn yayi wajen awanni bakwai a rufe a cikin kasa kafin a samu damar ceto shi. An garzaya da jaririn zuwa asibiti mafi kusa inda yake karbar kulawar ma’aikatan lafiya.

Wannan na nuna babu wanda ya isa ya kauce kaddararsa, domin kuwa kaddara tsarin Ubangiji ce ba mutum ba.

A wani labari da Legit.ng ta ruwaito, an ji kauyuka 67 a babban birnin tarayya Abuja, inda ake kashe tagwaye, zabiya da kuma yaran da mahaifiyarsu ta rasu wajen haihuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel