Gwamna ya yi hawaye yayinda ya ganewa idonsa fashewar tankar mai

Gwamna ya yi hawaye yayinda ya ganewa idonsa fashewar tankar mai

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, a ranar Juma'a ya zubar da hawaye yayinda yaga wadanda suka jikkata a gobarar fashewar tankar mai a karamar hukumar Ota ta jihar.

Yayinda yake jajintawa iyalan wadanda suka jikkata a asibiti, Abiodun ya bayyana cewa gwamnonin jihar Legas da Ogun, na shirin kawo karshen asarar rayuka a hanyar.

Abiodun ya bada umurnin kaisu asibiti a Legas da Abeokuta kuma ya yi alkawarin dauke nauyin kudin asibitin.

Mun kawo muku rahoton cewa Akalla mutane biyu sun rasa rayukansu, motoci 17 sun kone yayinda watar tanka mai dauke da man fetur ta samu hadari kuma ta kama da wuta a Sango, unguwar Ota, jihar Ogun cikin daren Alhamis, 14 ga Nuwamba, 2019.

KU KARANTA: Bayan kwanaki 19, Shugaba Buhari ya dawo Najeriya (Bidiyo)

Wuta ya babbaka mutanen biyu fiye da yadda za'a iya ganesu; hakazalika mutane shida sun jikkata.

Sakta kwamandan hukumar kiyaye hadura wato FRSC, Clement Oladele, ya yi bayani a jawabin da ya saki cewa annoban ya auku ne sakamakon matsalar da tankar man ta samu a kan hanya inda ta kife kuma mai ya zube.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel