Ana zaton wuta a makera: Dansanda ya yi ma diyar Yarsanda fyade a cikin barikin Yansanda

Ana zaton wuta a makera: Dansanda ya yi ma diyar Yarsanda fyade a cikin barikin Yansanda

Wata jami’ar rundunar Yansandan Najeriya ta shigar da karar wani jami’in dansanda abokin aikinta mai suna Mohammed Alidu gaban kotun hukunta laifukan fyade ta jahar Legas a kan tuhumarsa da yin lalata da diyarta a cikin barikin Yansanda.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito Yarsandan ta tabbatar ma kotu cewa a ranar da lamarin ya faru, Sajan Alidu ya raka diyarta zuwa gida ne daga makaranta, yayin da suke kan hanya kuma ya ja ta zuwa dakinsa, inda ya yi mata fyade.

KU KARANTA: Miyagun makiyaya sun halaka mutane guda 4 a jahar Kaduna

“Muna zama a barikin Makinde, Mafoluku dake yankin Oshodi na jahar Legas. A ranar 29 ga watan Yunin shekarar 2018 ina wajen aiki kwatsam sai mijina wanda baya gari ya kirani ya shaida min cewa Sajan Alidu ya zakke ma diyarmu.

Nan da nan zarce ofishin Yansanda dake cikin barikin, inda na tarar da diyarmu, kuma ta shaida min cewa tana dawowa daga makaranta ne sai Alidu ya kirata, amma ta ki amsa mai, amma sai da ya biyo ta, ya dauke da karfin tuwo zuwa dakinsa.

“Daga nan ya daurata a kan gadonsa, ya yaga dan bantenta sa’annan ya yi lalata da ita. Ko a lokacin da nake tare da diyata a ofishin Yansandan, Alidu na cikin ofishin DPO yana rokonsa afuwa, yana magiyan wai aikin shaidan ne.” Inji ta.

Yarsandan ta bayyana ma kotu cewa koda aka garzaya da diyarta zuwa wani asibitin Mirabel center, a can ma kwararrun likitoci sun tabbatar da cewa an yi mata fyade. Sai dai matar ta tabbatar ma kotun cewa Alidu ba shi da daki, a shago yake kwana.

Ita ma wata jami’ar Yarsanda, Sajan Juweratu Ashiru da ta bayar da shaida a shari’ar ta bayyana cewa a cikin dan shagon nasa suka kama Alidu bayan ya tafka laifin, kuma ya amsa laifinsa tare da neman su kashe maganar, su kuma suka ki.

“Hatta dan banten yarinyar sai da muka gano a cikin shagon, kuma muka daukeshi a matsayin hujja.” Inji ta.

A lokacin da kotun ta gayyaci yarinyar yar shekara 10 ta bayyana domin ta bayar da bayani, sai Alkalin kotun ya sallami duk masu zaman sauraron karar, domin a bata kariya, sa’annan bayan ta kammala bada jawabi ya dage karar zuwa ranar 15 ga watan Janairun 2020.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel