Zaben gwamna: Majalisar Dokoki ta jihar Bayelsa ta nemi a saka 'Dokar ta Baci'

Zaben gwamna: Majalisar Dokoki ta jihar Bayelsa ta nemi a saka 'Dokar ta Baci'

- Majalisar Dokoki na jihar Bayelsa ta nemi a saka dokar ta baci a karamar hukumar Nembe

- Majalisar ta kuma bukaci a soke zaben da za a gudanar a gobe Asabar a garin na Nembe sakamakon kashe-kashen da aka yi a yau Juma'a

- Majalisar har ila yau ta yi kira ga hukumomin tsaro su gaggauta binciko wadanda ke da hannu cikin rikicin domin a hukunta su

Ana 'yan wasu awanni gabanin zaben gwamna, Majalisar Dokoki ta jihar Bayelsa ta amince da kudirin neman saka dokar ta baci a karamar hukumar Nembe tare da neman a soke zaben da za ayi a garin a gobe Asabar.

'Yan majalisar sun bayyana cewa sun dauki matakin ne duba da rikicin da ya barke yayin yakin neman zaben jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a Nembe da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama bayan harbe-harbe da aka yi.

An zartar da kudirin ne karkashin harkoki na kasa masu bukatar a dauki mataki a kansu cikin gaggawa da Honarabul Ben Ololo mai wakiltan mazabar Nembe ya gabatar a zauren majalisar. Ya ce zubbar da jinin da aka yi a mazabarsa alama ce dake nuna cewa ba za a iya gudanar da zabe mai na adalci ba.

DUBA WANNAN: Bidiyon wani almajiri yana Sallah a kan dakalin coci ya dauki hankulan mutane

Dan majalisar ya yi tir da siyasar a-mutu-ko-ayi-rai da wasu 'yan siyasa masu son kai a jihar ke yi duk da bai ambaci sunansu ba. Honarabul Ben Ololo ya yi kira ga hukumomin tsaro a jihar su yi gaggawan daukan mataki kamo wadanda suka aikata mummunan lamarin domin a hukunta su.

Sauran takwarorinsa 'yan majalisa sun goyi bayan kudirin inda suka amince da kirarsa ta neman saka dokar ta baci a Nembe tare da soke zaben na gobe Asabar a karamar hukumar kamar yadda Linda Ikeji Blog ya ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel