Yanzu-yanzu: Bayan kwanaki 19, Shugaba Buhari ya dawo Najeriya (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: Bayan kwanaki 19, Shugaba Buhari ya dawo Najeriya (Bidiyo)

Bayan kwanaki daya-daya har goma sha tara a kasar Saudiyya da birnin Landan, shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya da daren Juma'a, 15 ga watan Nuwamba, 2019.

Buhari ya dira babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe ne misalin karfe 9 na dare.

Hadimin shugaba Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya bayyana bidiyon dawowar shugaban kasan ne a shafinsa na Tuwita.

Shugaban kasa Buhari, ya bar Abuja zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiyya inda ya halarci na masu saka hannu jari (FII) da hukumar samar da kudaden kasuwanci ta kasar Saudiyyya (PIF) ta shirya.

KU KARANTA: Zaben Kogi: Wata jam'iyya tana baiwa ma'aikatan INEC cin hancin Dala dubu daya-daya

An gudanar da taron ne daga ranar 29 ga wata zuwa ranar 31 ga watan Oktoba, kuma an tattauna ne a kan harkokin bunkasa kasuwanci ta hanyar fasahar zamani.

Shugaba Buhari ya samu rakiyar gwamnan Babagana Umara Zulum na jihar Borno, gwamna Abubakar Bagudu na jihar Kebbi da gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina.

Bayan halartan taron karfafa tattalin arziki a Saudiyya, shugaba Muhamadu Buhari ya garzaya kasar Ingila da sunan ziyarar kansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel