Zaben Kogi: Wata jam'iyya tana baiwa ma'aikatan INEC cin hancin Dala dubu daya-daya

Zaben Kogi: Wata jam'iyya tana baiwa ma'aikatan INEC cin hancin Dala dubu daya-daya

Cibiyar raya demokradiyya wato Centre for Democracy and Development (CDD) ta ce wata jam'iyya na baiwa jami'an hukumar zabe INEC a jihar Kogi cin hancin $1,000 wanda yake kimanin N365,000.

Kungiyar CDD ta saki jawabi ranar Juma'a cewa jami'anta da ta tura wurare daban-daban a sassan jihar sun tabbatar da wannan labari.

Jawabin ya ce wasu yan kasuwan canji sun samu kasuwa a yau inda ake kiransu domin canjin dalar Amurka dubu daya zuwa Naira.

A cewar CDD: "Akwai alamun cewa an ajiye makudan kudade domin sayen kuri'u gobe Asabar."

"Tuni, jami'an lura da zabenmu na gan yadda ake rabawa mutane atamfofi da shinkafa a Lokoja da karamar hukumar Koton Karfe."

"Amfani da kudi domin jan hankulan mutane ya sabawa ka'idojin demokradiyya."

"CDD tana kiracga hukumomin yaki da rashawa musamman EFCC da ICPC su yi bincike kan wannan rahoto kuma su damke wadanda ke aikata wannan laifi."

DUBA WANNAN: Mutane 2 sun hallaka, motoci 17 sun kone, yayinda tankar mai ta kama da wuta

Legit.ng Hausa ta kawo muku jerin yan takaran zaben gwamnan jihar Kogi da abokan takararsu, Ga cikakken sunayen yan takarar da jam’iyyunsu:

1. Abdullahi Muhammed (Accord Party)

Abokin takara: Ibitoye Roseline Abosede

2. Muhammadul-Kabir Abdul-Wasiu (AAC)

Abokin takara: Abdulrahman Ibrahim

3. Medupin Ephraim (AD)

Abokin takara: Jibrin Mohammed Tenimu

4. Justina Dolapo Abanida (ADC)

Abokin takara: Ibrahim O. Yusuf

5. Ndakwo Abdulrahman Tanko (ADP)

Abokin takara: Tukura Joseph Jimba

6. Orugun Emmanuel Olorunmowaju (ANRP)

Abokin takara: Ahmed Sa'eed Baba

7. Bello Yahaya (APC)

Abokin takara: Onoja Edward David

8. Ibrahim Jibril Sheik (APGA)

Abokin takara: Durojaiye I Hassan

9. Bello Williams Dele (GDPN)

Abokin takara: Suleiman Mohammed

10. Victor Akubo (GPN)

Abokin takara: Muhammed Rabi Bela Ladidi (GPN)

11. Gabdulmalik Adama Mohammed (HDP)

Abokin takara: Adeboye Samuel Olu

12. Alfa Amos Oboy (JMPP)

Abokin takara: Olayemi Olakunle Emmanuel

13. Jimoh Amodu Yusuf (MAJA)

Abokin takara: Awoniyi Oyewole Omotayo Sunday

14. Muhammed Ibrahim Dangana (NCP)

Abokin takara: Umar Abdulazeez Usman Odegiri

15. Musa Atayi Wada (PDP)

Abokin takara: Samuel Bamidele Aro

16 Ukwumonu Joseph Idachaba (PPN)

Abokin takara: Isa Karimu Yakubu

17. Moses Itodo Drisu (PPP)

Abokin takara: Sule Isah Obewa

18. Ayodele Raymond Ajibola (PRP)

Abokin takara: Tahir Yaqub

19. Natasha Hadiza Akpoti (SDP)

Abokin takara: Adams Ogbeche Khalid

20. Abdulrazaq Baba Emeje (UDP)

Abokin takara: Onemayin Paul Oluwole

21. Abuh Sunday Omogami (UPC)

Abokin takara: Yakubu Isah

22. Shaibu Sani Seidi (YDP)

Abokin takara: Onimisi Adedayo Benson

23. Aisha Abubakar Audu (YPP)

Abokin takara: Suleiman Ozigi Ahmed

24. Suleiman Mohammed Mikhail (ZLP)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel