Matasan jihar Edo sun goyi bayan Obaseki, sun caccaki Oshiomhole

Matasan jihar Edo sun goyi bayan Obaseki, sun caccaki Oshiomhole

Matasan jam’iyyar APC na jihar Edo, sun goyi bayan gwamna Godwin Obaseki a kan kudirinsa na cafkar tikitin takarar gwamnan jihar a 2020.

Kungiyar ta ce, ta goyi bayan tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomhole ya samu shekaru 8 cikin kwanciyar hankali a ofishinsa. A don haka ne ba za su zuba ido suna kallon wata kungiya ko mutum ya takura wa Gwamna Obaseki ba.

A zantawar da ya yi da manema labarai a ranar Juma’a a Benin, shugaban matasan jam’iyyar APC na jihar, Valentine Asuen ya ce, Gwamna Obaseki ya taka rawar da ake tsammani a duk bangarorin jihar na tattalin arziki.

A yayin Magana akan wasikar da aka mika ga kwamitin aiki na kasa na APC a kan dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar, Anselm Ojezua, ya bukaci kwamitin da su yi watsi da wasikar saboda duk hannayen da aka saka na bogi ne.

DUBA WANNAN: Kotu ta umurci 'yan sanda su tsare shugaban jam'iyyar NCP na Katsina

“Gwamna Obaseki ya taka rawar gani a bangaren lafiya, ilimi, sufuri, shari’a da kuma daga kudin shigar jihar. A don haka ne ba zamu yadda shi ba,” a cewarsa.

Ya ce, jihar Edo ce jiha daya kacal da kananan hukumomi ke iya biyan alabshi ba tare da sun jira kudi daga tarayya ba. Ya ce, wadanda ke rikici da Obaseki su ne masu dumbuza daga kudin shigar jihar.

“Muna tare da Obaseki kuma zamu tabbatar da cewa ya samu goyon bayan da yake bukata. Jihar Edo ba zata lamunci komawa tsaka mai wuyar da ta fita ba. Ba zamu barsu su yi nasara ba,” in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel