Da duminsa: Mutane 2 sun hallaka, motoci 17 sun kone, yayinda tankar mai ta kama da wuta

Da duminsa: Mutane 2 sun hallaka, motoci 17 sun kone, yayinda tankar mai ta kama da wuta

Akalla mutane biyu sun rasa rayukansu, motoci 17 sun kone yayinda watar tanka mai dauke da man fetur ta samu hadari kuma ta kama da wuta a Sango, unguwar Ota, jihar Ogun cikin daren Alhamis, 14 ga Nuwamba, 2019.

Wuta ya babbaka mutanen biyu fiye da yadda za'a iya ganesu; hakazalika mutane shida sun jikkata.

Sakta kwamandan hukumar kiyaye hadura wato FRSC, Clement Oladele, ya yi bayani a jawabin da ya saki cewa annoban ya auku ne sakamakon matsalar da tankar man ta samu a kan hanya inda ta kife kuma mai ya zube.

A cewarsa, man fetur ya kwarara daga kantin Shoprite dake Ota har zuwa ofishin FRSC dake tasha inda akayi asarar motoci, da dukiyoyi da dama.

Ya ce an kai gawawwakin mutane biyun da suka kone babbar asibitin Ifo, yayinda aka garzaya da wadanda suka jikkata babbar Asibitin Ota, jihar Ogun.

Wannan ya biyo bayan gobarar da ta lashe gidaje uku da shaguna hudu jiya a garin Abeokuta inda akayi asarar dukiyoyin makudan kudi.

A cikin watan Oktoba, tankokin mai akalla biyu sun kama da wuta a garin Onitsha, jihar Anambara inda yan kasuwa suka kwashi asaran dukiyoyi.

DUBA NAN Buhari na hanyar dawowansa Najeriya daga Ingila

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel