Dattawan Kano za su goga gemu da gemu da ministan Buhari a kan wata babbar bukata

Dattawan Kano za su goga gemu da gemu da ministan Buhari a kan wata babbar bukata

Dattawan jahar Kano, sun yanke shawarar tura wakili zuwa ga ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola domin jin matakin da yake dauka game da tabarbarewar babbar titin da ta tashi daga Kano zuwa Gwarzo zuwa Dayi.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito shuwagabannin al’ummomin sun bayyana cewa: “Za mu kai kokenmu ga ministan ayyuka game da halin da hanyar Kano-Gwarzo-Dayi take ciki, wanda a yanzu haka ta zama hanyar mutuwa.”

KU KARANTA: Dan daba ya shiga har cikin makaranta ya kashe wani dalibi a gaban Malamansa a Kaduna

Wakilin mazabar Gwarzo a majalisar wakilai, Yunusa Haruna Kauyu ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a birnin Kano a ranar Juma’a, 15 ga watan Nuwamba.

A cewarsa, tawagar dattawan Kano za ta kunshi har da kwamishinan ayyuka na jahar Kano, Alhaji Muazu Magaji, Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibrin Maliya tare da sauran wakilan al’ummar yankin dake majalisar tarayya.

“Ya zama wajibi mu tattauna da minista domin mu bayyana damuwarmu da halin da hanyar take ciki, hanya ce mai matukar muhimmanci da ta hada Kano da jahohi guda 4, har ma da Nijar. A shekarar da ta gabata an cike ramukan kan hanyar, amma a yanzu sun sake fashewa.

“Babban abin da hanyar nan take nema shi ne a kankareta a sake ginata, ba wai cike ciken ramuka ba, don haka muke fatan gwamnati ta bayar da kwangilar aikin titin.” Inji shi.

Tun a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida aka gina titin daya hada Katsina, Sakkwato, Zamfara da jahar Kebbi, kuma tun wancan lokaci bai taba samun wani gyaran kirki ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel