Dan daba ya shiga har cikin makaranta ya kashe wani dalibi a gaban Malamansa a Kaduna

Dan daba ya shiga har cikin makaranta ya kashe wani dalibi a gaban Malamansa a Kaduna

Rundunar Yansandan jahar Kaduna ta tabbatar da kama wani gagararren dan daba mai suna Sani Umar sakamakon tuhumarsa da ake yi da laifin kisan kai bayan ya kashe wani dalibin makarantar sakandari mai suna Hassan Abdullah.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Sani Umar ya kashe Hassan ne a ranar Alhamis, 14 ga watan Nuwamba a lokacin da ya shiga har cikin makarantar sakandari ta Rigachikun dake cikin karamar hukumar Igabi, inda ya soka masa wuka a gaban malamansa.

KU KARANTA: Zakzaky ya fi kaunar cigaba da zama a ofishinmu a kan zaman Kurkuku – DSS

Kaakakinn rundunar Yansandan jahar Kaduna, Yakubu Sabo ya tabbatar da aukuwar lamarin mai muni, inda yace Sani ya aikata wannan mugun aiki ne da misalin karfe 11 na safiyar Alhamis, inda Hassan ya mutu a kan hanyar kai shi asibiti.

Haka zalika kaakakin Yansandan Kaduna ya tabbatar da kama Sani Umar, ya kara da cewa a yanzu suna cigaba da gudanar da cikakken bincike game da lamarin, sa’annan an mika maganan zuwa ofishin Yansanda masu binciken manyan laifuka.

Daga karshe kaakakin yace zasu gurfanar da Sani a gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike, a kansa.

A wani labarin kuma, babban sufetan Yansandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu ya aika da sabbin kwamishinonin Yansanda zuwa wasu jahohin Najeriya guda 7 domin samar da ingantaccen tsaro a cikin jahohin da kewayensu.

Ga sunayen sunayen sabbin kwamishinonin da jahohinsu kamar haka; Habu Sani Ahmadu jahar Kano, Lawal Jimeta jahar Edo, Phillip Sule Maku jahar Bauchi, Nkereuwem A Akpan jahar Cross Rivers, Kenneth Ebrimson jahar Akwa Ibom, Odumusu Olusegun jahar Legas da Imohimi Edgal jahar Ogun.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel