Zakzaky ya fi kaunar cigaba da zama a ofishinmu a kan zaman Kurkuku – DSS

Zakzaky ya fi kaunar cigaba da zama a ofishinmu a kan zaman Kurkuku – DSS

Hukumar tsaro ta sirri, DSS, ta bayyana babban dalilin da yasa take cigaba da rike tsohon mashawarcin shugaban kasa a kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki, shugaban yan Shia Ibrahim Zakzaky da kuma jagoran juyin juya hali na RevolutionNow, Omoyele Sowore.

Idan za’a tuna DSS ta ki sakin wadannan mutanen uku duk kuwa da cewa suna fuskantar shari’u a kotuna daban daban a Najeriya, sai dai hukumar tace mutanen sun gwammace su cigaba da zama a hannun DSS fiye da zaman gidan yari.

KU KARANTA: Ashshsa! Jirgin rundunar dakarun Sojan saman Najeriya fado a jahar Enugu

Kaakakin hukumar DSS, Peter Afunanya ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, inda yace Zakzaky, Dasuki da Sowore ne suka roki kotu da ta taimaka ta barsu su cigaba da zama a hannun DSS a maimakon a mikasu zuwa Kurkuku.

A cewar kaakakin, “A wajenmu suna samu daman ganawa da mutanensu, kuma suna amfani da wayoyon salula, suna kallon talabijin, suna karatun jaridu, suna da daman shiga dakin motsa jiki, suna samun kulawa a asibitinmu sa’annan iyalansu na kawo musu abinci, babu inda zasu more kamar haka

“Don haka ba gaskiya bane a ce wai mun yi ma umarnin kotu karan tsaye ne wajen cigaba da rikesu, da wannan za’a gane lallai su da kansu suka gwammace su cigaba da zama a hannunmu fiye da zaman kurkuku, ba don komai ba sai don kawai muna da isassun kayan aiki.

“Baya cikin tsarinmu mu yi ta cece kuce da wasu mutane ko wasu kungiyoyi, amma a yanzu bai kamata mu yi shiru ba saboda dole ne mu yi ma yan Najeriya bayanin halin da ake ciki domin kowa ya fahimci gaskiyar lamarin.” Inji shi.

Daga karshe kaakakin yace hukumar DSS za ta cigaba da aiki hannu da hannu da kafafen watsa labaru da yan jaridu wajen ilimantar da jama’a game da ayyukanta, haka zalika za su cigaba da gudanar da aikinsu daidai da tanade tanaden dokokin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel