Yanzu-yanzu: Buhari na hanyar dawowa Najeriya daga Ingila

Yanzu-yanzu: Buhari na hanyar dawowa Najeriya daga Ingila

Shugaba Muhammadu Buhari na hanyarsa na dawowa Najeriya daga birnin Landan, kasar Ingila yanzu haka. Premium Time sta bada rahoto.

Jirgin shugaban kasa ya tashi daga filin jirgin saman Stansted dake Landan ne misalin karfe 3:27 na rana.

Majiya daga fadar shugaban sun bayyana cewa an umurcesu su kasance a filin jirgin saman Abuja daga misalin karfe 7:30 na dare domin tarban shugaban kasan da ake sa ran saukarsa misalin karfe 9 na dare.

Bayan halartan taron karfafa tattalin arziki a Saudiyya, shugaba Muhamadu Buhari ya garzaya kasar Ingila da sunan ziyarar kansa.

Daga can Landan, Buhari ya rattaba hannu kan muhimmin dokar karin harajin masu hakar arzikin man fetur a cikin teku. Hakazalika ya sallami hadiman mataimakin shugaban kasa 35.

Shugaban kasa Buhari, ya bar Abuja zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiyya inda ya halarci na masu saka hannu jari (FII) da hukumar samar da kudaden kasuwanci ta kasar Saudiyyya (PIF) ta shirya.

An gudanar da taron ne daga ranar 29 ga wata zuwa ranar 31 ga watan Oktoba, kuma an tattauna ne a kan harkokin bunkasa kasuwanci ta hanyar fasahar zamani.

Shugaba Buhari ya samu rakiyar gwamnan Babagana Umara Zulum na jihar Borno, gwamna Abubakar Bagudu na jihar Kebbi da gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel