Kotu ta umurci 'yan sanda su tsare shugaban jam'iyyar NCP na Katsina

Kotu ta umurci 'yan sanda su tsare shugaban jam'iyyar NCP na Katsina

A ranar juma’a ne kotu ta bukaci hukumar ‘yan sanda dasu cigaba da tsare shugaban jam’iyyar NCP reshen jihar Katsina, Kwamared Abdulmumini Shehu Sani. Kotun ta umarci hukumar ‘yan sandan ne da yin hakan biyo bayan yanke hukunci da ta yi akan daya daga cikin tuhume-tuhumen da ake masa.

An gurfanar da Sani ne a ranar Juma’a bayan da ‘yan sanda suka cafkesa a ranar Laraba. Ana zarginsa da bata suna, kazafi tare da rashin biyayya ga gwamnati, wanda abin hukuntawa ne a karkashin sashi na 392, 393 da 416 na dokokin Penal code.

A ranar Juma’a da aka fara sauraron karar, lauyan wanda ake zargi, Chukwuemeka Kalu ya musanta cewa, daya daga cikin zargin da ake wa wanda yake karewa ba zai yuwu kotun ta sauraresa ba saboda hade yake da laifin sukar gwamnati.

Ya jaddada cewa, bai kamata kotun ta saurara ba har sai an gyara karar.

DUBA WANNAN: Aisha Buhari ta fadi abinda ya hana Gwamna Bello biyan albashi a watannin a baya

A hukuncin alkalin, Nura Abdullahi, ya sa ranar 25 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a cigaba da shari’ar. Ya kuma bukaci hukumar ‘yan sanda da su cigaba da tsare wanda ake zargin har zuwa ranar.

Idan ba zamu manta ba, an cafke Sani sakamakon taron manema labarai da ya shirya a ranakun karshen mako. Ya zargi gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari da yunkurin ba wa alkalin kotun sauraron kararrakin zabe na jihar cin hanci, zargin da tuni gwamnatin jihar ta musanta.

Jami’an gwamnati da ‘yan siyasa masu yawa a jihar sun bukaci da a cafkesa tare da gurfanar dashi gaban kotu don bada gamsassun dalilai a kan wadannan zarge-zargen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel