Ko babu kwalin kammala karatun sakandare, Buhari ya cancanci takarar shugaban kasa - Kotun Koli

Ko babu kwalin kammala karatun sakandare, Buhari ya cancanci takarar shugaban kasa - Kotun Koli

Kotun kolin Najeriya ta bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi daidai wajen rashin baiwa hukumar gudanar da zaben ta kasa wato INEC kwalayen karatunsa.

Kotun ta bayyana hakan ne yayinda take zayyana dalilan da yasa tayi watsi da karar jam'iyyar PDP da dan takararta, Atiku Abubakar, a ranar Juma'a, 15 ga Nuwamba, 2019.

Manyan Alkalan sun yi ittifakin cewa ko babu kwalin karatu shugaba Buhari ya cancanci takarar kujeran shugaban kasa.

Kotun ta yanke cewa sabanin abinda PDP take ikirari, babu dokar da ta bukaci dan takara ya gabatar da kwalayen karatunsa ga hukumar INEC kafin ta amince yayi takara.

Hakazalika kotun ta bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya bai wajabtawa dan takara mallakan kwalin karatun sakandare. Abinda kawai doka ta bukata shine ya halarci makarantar sakandare ko bai kammala ba.

Ta ce shugaba Buhari ya halarci sakandare kuma da kwalinsa, ya kai matsayin manjo janar a hukumar Soji, ya samu horon ilmin yaki, ya zama shugaban kasar nan, ya iya magana da fahimtar yaren turanci kuma yanada kwalin kammala karatun firamare; dukkan wadannan sun isar.

Bisa ga wadannan dalilai, Justice Inyang Okoro a madadin kotun tayi watsi da lamarin zargin cewa Buhari bai yi karatun sakandare ba kuma saboda haka bai cancanci takara ba.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel