An kama wata mai fataucin miyagun kwayoyi a cibiyar tsare masu laifi na Kano

An kama wata mai fataucin miyagun kwayoyi a cibiyar tsare masu laifi na Kano

Hukumar gidan gyara halayyar dan adam wato kurkuku reshen jihar Kano, ta kama wata bakuwa wacce aka sakaya sunanta a cibiyar. An tattaro cewa bakuwar ta yi kokarin fasa kaurin wasu haramtattun kayayyaki ne lokacin da aka cafke ta.

Mataimakin Shugaban reshen gidan gyaran halayyan, DSC Musbahu Lawan, wanda ya bayyana hakan a wani jawabi a Abuja a ranar Juma’a, 15 ga watan Nuwamba, ya ce ana zargin kwayoyin Diazepam ne ta shiga dashi cibiyar..

Mista Lawan ya bayyana cewa an kama matashiyar mai shekaru 20 daga Hotoro Quarters, karamar hukumar Nassarawa da ke jihar Kano dauke da miyagun kwayoyi da ya kai N300,000 ayinda ta ke kokarin fasa kaurinsa zuwa cikin cibiyar.

Ya bayyana cewa an nade kwayoyin ne cikin miyar wani fursuna da ke jiran shari’a a cibiyar.

DSC din ya bayyana cewa an cafke ta ne a kofar gidan kurkukun lokacin da ake incike yayinda ta kawo wa fursunan abinci.

“Daga bisani ta tona cewa wani mutum da bata sani bane ya bata kayayyakin domin ta isar dashi zuwa ga fursunan da ke jiran shari’a,” in ji shi.

Mista Lawan ya bayyana cewa tuni aka mika ta zuwa ga jami’an hukuma hana fatauci da shan miyagun kwayoyi, NDLEA domin cigaba da bincike.

Mataimakin kwanturola na gidan kurkukun, DCC da ke kula da hukumar, Irahim Idris ya ce kwayoyin da ake Magana a kai da zai shafi kwakwalwa da lafiyar fursunan idan da ya samu shiga ciki.

KU KARANTA KUMA: WAEC ta saki sakamakon jarrabawa, ta ce mutane 33,304 cikin 94,884 ne suka lashe darusa 5

Hakazalika kwanturolan kurkuku, reshen jihar Kano, Magaji Abdullah, ya nuna farin ciki kan gano miyagun kwayoyin da aka yi.

Mista Abdullahi ya shawarc jami’an hukumar da su kara ninka kokarinsu wajen hana miyagun Kwayoyi shiga cibiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel