Yanzu-yanzu: 'Yan ta'adda da fuska a rufe sun kaiwa Gwamna Makinde hari a Kogi (Hotuna)

Yanzu-yanzu: 'Yan ta'adda da fuska a rufe sun kaiwa Gwamna Makinde hari a Kogi (Hotuna)

Ana zargi wata kungiyar jami’an tsaro dauke da makamai kuma fsukokinsu rufe, sanye da kayan jami’an ‘yan sanda da kaiwa gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde a otal din Lokoja dake jihar Kogi.

Hakan na kunshe na a takardar da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Taiwo Adisa, yasa hannu.

Yanzu-yanzu: 'Yan ta'adda da fuska a rufe sun kaiwa Gwamna Makinde hari a Kogi

Yanzu-yanzu: 'Yan ta'adda da fuska a rufe sun kaiwa Gwamna Makinde hari a Kogi
Source: UGC

Yanzu-yanzu: 'Yan ta'adda da fuska a rufe sun kaiwa Gwamna Makinde hari a Kogi

Yanzu-yanzu: 'Yan ta'adda da fuska a rufe sun kaiwa Gwamna Makinde hari a Kogi
Source: UGC

Takardar ta ce: “Bayanan da suke iskemu daga Lokoja, babban birnin jihar Kogi sun tabbatar mana da cewa, wasu jami’an tsaro dauke da makamai kuma fuskarsu a rufe sun hari gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde a Lokoja, jihar Kogi.

“Makinde shi ne shugaban kungiyar yakin neman zaben jam’iyyar PDP a jihar Kogi. Ya je jihar ne a matsayinsa na shugaban kungiyar.

“Ganau ba jiyau ba sun tabbatar mana da cewa, jami’an tsaron sun bayyana ne a Suitorial hotel dake Lokoja, wanda yake kan titin filin was an jihar, inda gwamnan da wasu mambobin kungiyar kamfen din suka yi masauki. Da misalin karfe 12:50 na ranar Juma’a ne suka ji harbe-harbe ba kakkautawa kuma mutanen suka yi kokarin ballowa su shiga dakunan otal din.

DUBA WANNAN: Nesa ta zo kusa: Garin da a ke aure da N50,000 kacal

Yanzu-yanzu: 'Yan ta'adda da fuska a rufe sun kaiwa Gwamna Makinde hari a Kogi

Yanzu-yanzu: 'Yan ta'adda da fuska a rufe sun kaiwa Gwamna Makinde hari a Kogi
Source: UGC

“Kamar yadda muka samu labari, mutanen da a ke zargin, sun tsallake katangar otal din tare da yunkurin shiga dakunan. Tuni jami’an tsaron dake tare da Gwamnan suka yi garkuwa inda suka fi karfin masu kutsen.

“A cikin kankanin lokaci, wasu mazauna yankin suka taya jami’an tsaron gwamnan inda aka fi karfin masu kutsen.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel